Abubakar Abba" />

Kudin Shiga: Hakilon Gwamnatin Kaduna Na Neman Masu Son Zuba Jari

Daga Abubakar Abba, Kaduna

Taron shekara na zuba jari da gwamnatin jihar  Kaduna ta gudanar a kwanan baya a cikin jihar, yana da mahimmancin gaske wajen habaka tattalin arzikin jihar, amma sai dai cin amfanin wannan yunkurin, ya danganta ne akan yadda gwamnatin jihar ta jajirce wajen magance turnikin rashin tsaro da ya yiwa wasu sassan jihar daurin Demon Minti.

Jihar Kaduna tana akan gaba wajen hada-hadar kasuwanci da yawn masana’antu, musamman wadanda suke a Arewacin jihar baya ga jihar Kano.

Jihar tana da komai da zata iya yanyo  hankalin ‘yan kasuwa da kuma masu sun zuba jari.

Amma sai dai, ga dukkan alamu tana fuskantar rashin mayar da hankali wajen samar da kyakyawan yanayi don a zuba jari a jihar.

Gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufai tana kokari wajen canza wannan yanayin musamman ganin cewar jihar Allah ya albarkace ta da dimbin ma’adanai da aikin noma da kuma alumma.

El-Rufai, a 2016 ya kirkiro da taron zuba jari a jihar mai suna (KADINBEST),  inda taron yake bai wa masu son zuba jari damar zuba jarin su a jihar.

Sanannun manyan kasuwa dake kasar nan dana kasashen waje sun halarci taron karon farko da gwamnatin jihar ta shirya.

SAKAMAKO:

Taron ya yi bufin bayyana albarkantun da jihar keda shi wadanda kuma ba a riga an tono su ba.

Bayan samun cin nasarar gudanar da tarurrukan har kashi uku a jihar, ga dukkan alamu taron ya fara haifar da da mai ido.

A cewar tsohon Babban Sakatare ES na hukumar (KADIPA) mallakar gwamtin jihar Alhaji Gambo Hamza, taron ya kara bunkasa matsayin tattalin arzikin jihar a idon duniya.

Tarin karo na uku, an gudar dashi ne a ranar 4 ga watan Afirili taron na karo na biyar, ya samu halarcin ‘yan kasuwa maza da mata na gida da kuma na wajen kasar nan, harda tsohon shugaban kasar Tanzania, Dakta Jakaya Kikwete.

Da yake jawabin sa akan tagomashin da taron yake dashi, El-Rufai ya bayyana cewar, burin sa na mayar da jihar wajen samun damar amfanar ‘yan Jihar akan dimbin  albarkatun tattalin

arziki da take dashi.

A cewar El-rufau, “fatan mu shine nan da shekarar 2020, Kaduna zata zama jihar da ‘yan kasuwa zasu dinga zuwa don zuba jari kuma ta zamo jihar dake samar da abinci a Arewacin Nijeriya, inda kuma daukacin ‘yan jihar zasu samu ingantaccen ilimin zamani, a saboda haka muna zuba jari akan alummar jihar”.

Ya ci gaba da cewa, a tarurrukan na zuba jari da aka gudanar,   a cikin shekaru biyu, tun lokacin da aka kaddamar da taron na(KADINBEST), masu sun zuba jari a jihar sun amsa kira ta hanyar kakkafa kasuwanci a jihar.

Daya daga cikin irin wannan zuba jarin, shine kafa babban masana’antar kiwon Kaji da sarrafa abincin dabbobi na nahiyar Afirka na Olam dake kasar  Singapo ya zuba jarin dala miliyan 150, inda kuma hakan zai samar da ayyukan yi kai tsaye kimanin 10,000.

Ya kara da cewa, masana’antar wanda yake a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, ya samar da kayan aiki da suka  na naira biliyan 20 kuma shugaban kasa  Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da ita a ciki watan Satumbar 2017.

El-rufai ya kara da cewa,“a yanzu haka mun samu nasarar janyo masu zuba jari da kuma samar da gidaje masu saukin kudi da suka kai kimanin  Dala biliyan 100.

Ya bayyana cewar, har ila yaun akawai manasa’anta ta Bicampro dake gudanar da kasuwancin aikin noman wadda itace mafi girma wajen noman Tumatir da kua sarrafa shi a jihar, inda aka zuba jari na kimanin dala dala biliyan 100.

A cewar El-rufai, “mun jawo hankalin masu zuba jari da zasu juba jarin dala miliyan 40  ga cibiyoyi mallakar gwamnatin jihar da kasuwanni a daukacin fadin jihar, inda hakan zai samar da ayyukan yi samada 2, 000”.

Ya bayyana cewar, sauran zuba jarin da gwamnatin ta samar a jihar sun hada da; masana’atar hada Taraktocin noma na Mahindra dake kasar Indiya wanda zai harhada taraktoci ga jihar da Nijeriya da kuma sauran kasuwanin dake Afrika ta Yamma.

El-rufai ya ci gaba da cewa, akwai kuma masana’atar Sunseed ta sarrafa abincin dabbobi dake Zaria,inda aka zuba jarin dala miliyan 10, kuma masana’antar zata samar da ayyukan yi kimanin 300, ya kara da cewar, akwai kuma masana’atar sarrafa Tumatir daje garin Jos data dawo kaduna.

A cewar sa, muna kuma da cibiyar fannin samar da bayanai kimiyyya ta zamani wadda aka zuba jarin dala miliyan 5.

Har ila yau, gwamnan ya ce, akwai masana’antar Blue Camel Energy dake hada na’urorin samar da hasken wutar lantarki da rana a Kaduna wadda aka zuba jarin dala 200,000.“

Ya sanar da cewar, “muna da irin wannan damar ta zuba jarin kasuwanci da a yanzu ake kan ci gaba da yi tun lokacin da aka kirkiro da taron.”

Ya ce, taron karo na farko da aka gudanar a 2016, ya mayar da hankali ne wajen ciyar da Kaduna gaba ta hanyar samar da tsare-tsaren na tsawon shekaru biyar masu zuwa da kuma mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga ‘yan jihar.

A cewar sa,“fatan mu shine, kafin zuwan 2020, Kaduna zata zamo iyaka ta zuba jarin kasuwanci da samar da abinci ga Arewacin Nijeriya, inda daukacin alummar jihar, gwamnati zata wadata su da ingantaccen ilimin zamani.

Ya yi kirdado akan tsare-tsaren habaka tattalin arzikin jihar na shekaru biyar masu zuwa don zuba jari da ya kai sama da naira biliyan 800 da ake tsimayi.

A cewar sa, “zan iya cewa, dukkan taron mu na son zuba jari a jihar, ba taron shan shayi bane.”

El-rufai ya sanar da cewar, kimanin kashi  79 bisa dari na masu son zuba jari da gwamnatin ta janyo, ‘yan kasar waje nen inda kuma kasha 21 bisa dari, na cikin gida ne.

A cewar sa, “muna son mu mayar da hankali akan masu zuba jari na cikin gida kuma tuni mun fara gudanar da ayyuka da nufin inganta rayuwar alummar jihar.

TSIMAYI:

El-Rufai ya bayyana cewar, sauran zuba jarin suna a kan hanya da zasu iso gaha masakar dake Jamus.

A cewar sa, “ muna kan tattaunawa da da kamfanin na Belisco, dake Jamus don samar da masaka don farfado da masakar dake Kaduna.”

Ya ci gaba da cewaan “muna kuma kan gudanar da aiki da kamfanin Alam, daya daga cikin kamfanonin dake sarrafa Madara a duniya don fara gudanar da masana’atar sarrafa Madara a Kaduna.”

El-rufai ya kara da cewar,“har ila yau, muna akan gudanar da aiki da Zailani Aliyu don kafa samar da inda za a dinga gyaran motoci na zamani.”

Ya sanar da cewar, “muna kokarin kafa kamfani da zai baiwa manoman sukunin sayar da amfanin gonar su.”

Ya sanar da cewar, “muna gudanar da aiki da masu zuba jari don gina manyan otel din guda biyu a  Kaduna.”

El-rufai ya bayyana cewar, “mun kusa kammala shirye-shirye don fara gina Asibiti da zaici gadaje 200 a otek din Hilton dake Kaduna.”

A cewar sa, muna kan gudanar da aiki da kamfanin Dangote da Kamfanin harhada motocin PAN don samar da sabon kamfanin Dangote na PAN na harhada motoci.

A cewar El-rufai, Kaduna tana bukatar kimanin dala biliyan 65.6 don zuba jari akan kayan aiki daga yanzu zuwa 2050.

KUDIN SHIGA:

Sama da shekaru biyu da suka shige,  kudin shiga na jihar ya karu, inda alal misalin, a 2017 an samu naira biliyan  26.53.

Shugaban hukumar tara harajin na Kaduna (IRS) Mukhtar Ahmed, ya sanar da cewar, alkalamun sun kai kashi 52 bisa dari, inda yake nuna ya kai naira biliyan 50.2 da aka sa ran samu a shekarar, inda aka samu karin naira biliyan 3.5 daga cikin naira biliyan 23 da aka tara a 2016.

Ahmed added that the sta ya kara da cewar, kudin shiga da aka sa ran samu, sun kai naira biliyan 42 a 2018.

Shi kuwa tsohon Shugaban kasar  Tanzaniya Kikwete a nashi jawabin ya yi nuni ne da cewar, samar da kyakyawan yanayi shine babban ginshiki da zai baiwa masu son zuba jari kwarin gwaiwa suzo su zuba jari.

Shima a nashi jawabin Ministan Ma’aikatar Jirga-zirga Chibuike Amaechi, ya shawarci masu son zuba jari a jihar kada su razana akan sace mutane da ake yi a wasu sassan kasar nan, inda ya yi nuni da cewar, zuba jarin zai samar da ayyukan yi da rage aikata manyan laifukka.

RASHIN TSARO:

Sai dai, masu yin suka da dama, basu gamsu da zuba jarin da taron yake shelar masu son zuba jarin su zuba jarin su a  jihar ba, duk da ikirarin da da jihar take yi na cewar tana da dimbin ma’adanan da ba’a tono su ba a jihar.

Kakakin jamiyyar APC na tawariyya dake jihar Murtala Abubakar, ya sanar da cewar, gwamnatin jihar bata samar da kyakywan yanayin da zai sanya masu son zuba jari zasu zo su zuba jarin su ba.

Abubakar ya yi nuni akan yadda alamuran aikata manyan laifuka suke kara karuwa a jihar, musamman masu sace mutanen da basu ji basu gani ba da sace Sahnu da masu kai hari, inda ya yi nuni da cewar, wadannan kawai sun isa su razana masu son zuba jari a jihar.

Ya yi nuni da cewarn “in har kana son samun asu zuba jari, dole sai ka samar da kyakyawan yanayi tukunna da kuma samar da wadataccen tsaron, domin ga dukkan alamu Kaduna tana cikin yanayi na rashin tsaro.”

Shugaban ya yi nuni da cewar, kaje Kudancin jihar, har yanzu akwai rashin tsaro haka a karamar hukumar Birnin Gwari da Kajuru da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da sauran hanyoyi, inda ake ta faman sace jama’a ba kakautawa a kullum, a saboda haka a cikin wannan yanayin zai yi wuya masu zuba jari suzo jihar don zuba dukiyar su.

Banda masana’antar Olam, ina kalubalantar gwamnatin jihar data nuna mana wani hobbasa da ta yi akan masu zuba jarin.

A cewar sa,”abinda a hakikanin gaskiya muke bukata bawai maganar taron zuba jari bane, amma kamata ya yi a shirya taron yadda za a tunkari magance matsalar rashin tsaro data dabai-baye jihar kamar sace mutane da satar Shanu da rikicin manoma da makiyaya, har sai idan an magance wannan ne sannan za ayi maganar nemo masu zuba jari.

A cewar Murtala, masana’antar  Bicampo ta sarrafa Tumatir da gwamna yake magana akai, inbestment,har yau bata fara gudanar da aiki ba.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewar, aikin ya tsaya cak, saboda tayar da kayar baya da alummar dake yankin suka tayar akan rikicin fili.

Sai dai, Sakataren roko na janiyyar  APC, mai mulki na jihar Yahaya Baba Pate, ya bayyana cewar, zuba jarin  had b taron na zuba jarin yana da babbar alfanu ga jihar.

A cewar sa, “muna zuba jari da ya kai na yawan miliyoyin dala da masan’antar sarrafa Tumatir na Bocampo ya yi a karanar hukumar Kaur da kuma na miliyoyin dala na kamfanin Olam ya zuba karamar hukumar Chikun, kuma ya kai aikin kimanin dala miliyan 150 na kiwon kaji a

Afrika.”

Ya kara da cewa,” muna da kamfanin sarrafa na’urorin masu aiki da hasken rana.

Ya yi nuni da cewar, dukkan wannan zuba jarin sakamakon taron da aka gudanar ne ya haifar dasu, haka gwamnati ta magance sace mutane da ake yi a jihar da kuma ayyukan ta’addanci na ‘Yan Sara-Suka.

A cewar sa, gwamnati tana iya kokarin ta don ganin ta kawo karshen aikata manyan laifuka a jihar, duk da dai cewar, harkar rashin tsaro babban kalubale ne da jihar ke fuskanta, musaman yawan sace mutane da kashe kashe da ake yi a babbar hanyar  Abuja da karamara hukumar Birnin Gwari da kuma wasu sauran sassan Kudancin Jihar.

Samun fitowar ‘yan Sara-Suka akan wasu titunan cikin  Kaduna, yana kara zamowa turniki.

Sai dai, anyi amannar cewar, za a janyo masu son zuba jari a jihar in har an dauki kwararan matakai na magance rashin tsaro a jihar.

Exit mobile version