Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Kula Da Al’umma: NAF Ta Gudanar Da Binciken Cutar Daji A Osun

by Muhammad
November 28, 2020
in LABARAI
3 min read
Cutar Daji
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mahdi M. Muhammad

A ci gaba da kokarin bunkasa alakar farar hula da sojoji, sojojin saman Nijeriya (NAF), sun kaddamar wa wani shirin kiwon lafiya kyauta na kwana 2, da kuma gwajin cutar daji ‘Cancer’ ga mutanen Ipetu-Ijesha, a karamar hukumar Oriade na jihar Osun.

Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, ayyukan binciken lafiya kyauta na cutar daji, wanda aka fara a ranar, 25 Nuwamba, 2020, kwatsam kuma sai ya hade da ranar cutar daji ta duniya.

Baya ga bayar da bayanai game da cutar daji da tantance mahalarta taron kiwon lafiyar, wanda wani shiri ne na Shugaban sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadique Abubakar, za kuma a ba da cikakkun ayyukan kiwon lafiya kamar, likitoci, dakin gwaje-gwaje, duba lafiyar ido da samar da tabarau a likitance, kula da hakora, lafiyar yara, bada magunguna kyauta, kuma har ma da kula da cutar zazzabin cizon sauro tare da samar da gidan sauro mai maganin kwari, da sauransu.

Da yake jawabi yayin taron kaddamar da tutar, Babban Bako na musamman (SGOH), Gwamnan Jihar Osun, Mista Adegboyega Oyetola, wanda Kwamishinan Kiwon Lafiya na jihar Osun, Dakta Rafiu Olasukanmi Isamotu ya wakilta, ya bayyana cewa, ayyukan binciken cutar daji da bada kiwon lafiya kyauta da ke gudana a jihar, alama ce da ke nuna irin ci gaban da NAF ke kawo wa, da kuma shawo kan zukatan al’ummomin da ke karbar bakuncin su a duk fadin kasar nan.

Ya kara da cewa, an gudanar da ayyukan ne domin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga mutane sama da 3,000. Don haka ya bukaci al’ummomin da ke karbar bakuncin su, yi amfani da damar da suka samu don biyan bukatun kula da lafiyarsu. Ya kuma roke su da su ba da hadin kai ga kungiyar likitocin NAF, don tabbatar da cewa an gudanar da atisayen cikin tsari don cimma babbar nasara.

Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa, Gwamnatin jihar Osun, a nata bangaren, za ta ci gaba da bayar da duk goyon bayan da ya kamata ga ayyukan NAF a cikin jihar.

Gwamna Oyetola ya kuma bayyana godiyarsa ga babban kwamandan askarawan Nijeriya, Shugaba Muhammadu Buhari, kan goyon bayan da yake bayarwa don bunkasa shirye-shirye da jin dadin rundunar sojojin Nijeriya, duk da halin tattalin arziki da ake ciki a kasar a halin yanzu.Ya kuma yaba wa jagoranci mai hangen nesa, himma, jajircewa da kwazo na shugaban NAF, a yayin gudanar da ayyukansa, wanda ya bayyana a matsayin abin koyi ga kowa. Gwamnan ya kara da cewa, burin shugaban shi ne maida NAF mafi kyawun hukuma a Afirka, wanda kuma tuni ya samar da ribar da ake nema.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Kwamandan Rundunar Sojan Sama (AOC), Kwamandan Ayyuka na musamman (SOC), Air Vice Marshal (ABM), Charles Ohwo, ya ce, aikin ginin na kasa nauyi ne na hadin kai, ya kuma bayyana cewa, NAF a karkashin shugabancin Air Marshal Abubakar, ta ci gaba da bayar da fifiko kan samar da ingantaccen kiwon lafiya da sauran aiyukan jin kai ga al’ummomin da ke karbar bakuncinsu, har ma da ‘yan gudun hijira a fadin kasar nan.

A ranar farko ta fara aikin kiwon lafiyar, an gabatar da jawabai akan cutar daji na Mara da na mahaifa ta bakin manyan Malamai, Farfesa Abdulkadir Salako da Dakta Akinfolarin Adepiti, yayin da aka gudanar da gwajin cutar dajin mahaifa da ta ‘Prostate’ ga kusan mutane 350 mambobi na alumma, kuma duk a lokaci guda tare da babban aikin likitanci ga sauran mambobin al’umma.

Da yake nuna farin cikinsa game da ayyukan, Mai Martaba Oba, (Dr) Samson Adeleke Agunbiade Oke, Agunbiade na III, Ajalaye na Ipetu Ijesha, ya yaba da shugabancin NAF na kawo irin wadannan ayyukan jin kai da na kiwon lafiya ga mutanen yankin. Ya kuma gode wa hukumar kan irin gudummawar da ta bayar wajen tabbatar da tsaro a Ipetu-Ijesha.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan shirin, Mista Olatumise Olawale, ya gode wa NAF da ta kawo musu dauki a daidai lokacin da kasar ke fuskantar koma baya na tattalin arziki. Ya kuma bayyana cewa, yana daya daga cikin wadanda suka sami kyautar gilashin ido da kuma magungunan hawan jini. Sauran mambobin jama’ar sun kuma nuna farin cikinsu da samun matukar alfanu daga ranar farko ta isar da aikin kiwon lafiyar.

Wadanda suka halarci taron kaddamarwar sun hada da mambobin da ke wakiltar mazabar Oriade da Ilesha ta Yamma, Honarabul Desmond Ojo da Wale Adedoyin, da kuma sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma tare da kwamandan tawaga ‘209 Kuick Response Group’ ta Ipetu-Ijesha da sauran manyan jami’an NAF.

SendShareTweetShare
Previous Post

#EndSARS: Kwamitin Bincike Ya Biya Mai Shigar Da Korafi Diyyar N150,000

Next Post

Hukumar Hisbah Ta Nemi A Daina Ambaton ‘Black Friday’

RelatedPosts

Da Dimi-diminsa: Buhari Ya Sauya Shugabannin Rundunonin Tsaro

Da Dimi-diminsa: Buhari Ya Sauya Shugabannin Rundunonin Tsaro

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da murabus din shugabannin...

Man Fetur

Kudirin Dokar Man Fetur Zai Bai Wa Nijeriya Damar Cin Gajiyar Albarkatunsa – Majalisar Dattawa

by Muhammad
15 hours ago
0

Daga Muhammad Maitela, Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan...

Jobe

Ma’aikata Da ’Yan Fansho Ke Wawashe Rabin Kudin Katsina, Cewar Kwamishina Jobe

by Muhammad
15 hours ago
0

Daga Sagir Abubukar, Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki...

Next Post
Hisbah

Hukumar Hisbah Ta Nemi A Daina Ambaton ‘Black Friday’

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version