Kulob Din Wikki FC Na Bauchi Ya Sayo dan Wasa Daga Kasar Waje

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bayyana cewar tun lokacin da gwamnatinsa ta dare kan karagar mulki a watan Mayun 2019 take samar da yanayi mai kyau da inganci wa harkokin kwallon kafa da sauran wasanni a fadin jihar domin bunkasa fannin.

“Na yi kokarin samar da kyakkyawar yanayi domin bunkasa harkokin wasanni domin tabbatar da harkokin wasanni sun je zuwa matakin da ya dace. Kuma ina karfafa musu guiwa sosai. Ni dattijo ne, amma duk da hakan ina nawa harkokin wasanni da motsa jiki a cikin gida, ma’ana dai ina zuwa gidan motsa jiki.”

Bala wanda ke jawabi a shekaran jiya lokacin da ya amshi sabon dan wasan kwallon kafa dan asalin kasar Egypt wanda kulub din Wikki Football Club da ke Bauchi ta sanya hannun yarjejeniya da shi wato Mahmood Saeed Gamal, Gwamnan ya nuna damursa na cewa kulob din Wikki bai tabuka abun azo a gani a wannan shekarar ba, sai ya jawo hankalinsu da su kara azama da himma domin ganin suna samun nasarar a gasar kwallon da suke shiga fafatawa.

Sanata Bala Muhammad ya kuma bayyana cewar ta harkar wassanni jiha ko kasa na samun daukaka a idon duniya da sanuwa, yana mai cewa “Kun sani ‘yan Nijeriya suna matukar son kwallon kafa, musamman yaranmu a Bauchi, kalibinsu ‘yan kwallon kafa ne.”

Bala ya yaba wa Manajan sabon dan wasan, Mista Philip Dosu, yana mai nuna cewa akwai kyakkyawar alaka tsakaninshi da Dosu, tun ma lokacin da yake Ministan Abuja.

Gwamnan ya yi farin ciki da sanya hannu da sabon dan wasan wanda kuluf din Wikki suka yi, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da biyan dan wasan alawus-alawus dinsa na sanya hannun harjejeniya.

Ya nemi dan wasan da ya tabuka abun a zo a gani domin daukaka darajar kulob din jihar, ya nuna kwarin guiwarsa na cewa tabbas za a samu ingancin wasan kwallon kafa sakamakon sanya hannun yarjejeniya da dan wasan kasar wajen.

Manajan dan wasan, Mista Philip Dosu, ya bada tabbacin cewa lallai Bauchi ta samu dan wasa mai kwazo da zai yi kokari wajen kyautata kulub din, yana mai cewa wannan matakin na zuwa ne bayan da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Wikki FC ya bayyana masa cewa kulob din na fama da matsalar rashin ‘yan wasa a wasu filolin.

Ya bayyana cewar an zabo Gamal ne bayan duba cancanta da cewarsa tare da taka ledar da aka tabbatar ya iya, don haka suke da yakinin zai zama dan wasan da jihar Bauchi za ta yi alfahari da shi matuka.

 

Exit mobile version