Kungiyar ‘Tansparent Leadership Advocacy’ (TLA) ta shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya mayar da hankali kan kudaden da ake kashewa a NNPC karkashin jagorancin Malam Mele Kyari.
Wata sanarwar manema labarai da shugaban kungiyar Dokta Musa Adam ya sanya wa hannu ta bayyana cewa an shirya shirin ne tun bayan dakatar da gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele.
Adam, a cikin sanarwar, ya bayyana cewar sabon shirin da kafafen yada labarai ke yi kan kamfanin NNPC da Mele Kyari, an kitsa ne tun bayan kaddamar da aikin hakar danyen mai a yankin Kolmani a Jihar Bauchi da Gombe) a ranar 22 ga watan Nuwamba.
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, “wasu marasa kishin kasa, sun bullo da sabon salo don shafa bakin jini ga kamfanin NNPC.
Kungiyar ta bayyana cewa “Kyari ya bullo da tsari don inganta mai nagarta a lokacin shugabancinsa. Duk wata NNPC na fitar da jadawalin kudaden da ake kashewa a kafafen yada labarai wanda ba taba yi ba a tarihin tattalin kasar nan.”
TLA, a cikin sanarwar ta kuma bayyana shugaban kamfanin NNPC a matsayin mutum mai tsattsauran ra’ayi, musulmi na musamman, wanda ke jajircewa wajen yin amfani da abin da yake da shi wajen hidimta wa marasa karfi.
Kungiyar ta bukaci shugaba “Bola Tinubu da ya yi watsi da kalaman wasu marasa kishin kasa da ke aiki da kafada da kafada da ’yan jarida don gogawa shugaban NNPC bakin jini a wajen Shugaba Tinubu, musamman a wannan mawuyacin hali da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki”.