Kungiyar Bayar Da Tallafi Ga Marayu Ta Tallafa Wa Marayu Sama Da Dubu Biyu A Legas

Daga Bala Kukkuru Legas

A ranar karamar sallar nan data wuce ne ta a zumin watan Ramadan na bana daya gabata a karshen makon nan daya shude na cikin wannan shekarar kungiyar bayar da tallafi ga marayu ta kasa akar kashin kungiyar izalatul bidia wa ikamatussun ta kasa kar kashin jagorancin shugaban ta shek Alhaji Dakta Bala lau kungiyar ta bayar da tallafin gamarayu reshen jihar Legas ta kira taron gudanar da walimar cinabincin salla da yara marayu sama da dubu biyu tareda tallafa masu da suturar sawa ta salla domin debe masu kewar iyayensu maza tamkar iyayen nasu suna raye a duniya baki daya.

Taron walimar cin abinci da yara marayun wanda ya hada da iyayen marayun mata da wadan su kusoshin kungiyar da sauran al’ummar musulmi wadanda suka je sallar idi tare da marayun gaba daya kuma taron walimar ya gudana ne a ofishin kungiyar dake Alfa lilla kan titin kafton wani waya jakshan Agege kuma taron gudanar da walimar ya samu halartar dumbin alummar musulmin da suka fito daga sassa daban daban dake cikin garin Legas a ranar sallar nan data gabata da yake nuna alhini tare da jin dadin sa shugaban kwamitin kungiyar na reshen jihar Legas Alhaji Ummar Lawan Agege inda ya cigaba da nuna farin cikinsa, ya ce lallai yana mai nuna farin cikin sa ga wannan rana ta salla da Allah ubangiji ya basu ikon gudanar da wannan taro na walimar cin abincin salla tare da yara marayu sama da dubu biyu domin a cire masu kewa ta iyayen su maza wadanda suka rigamu gidan gaskiya da fatan Allah ubangiji ya jikansu da rahama sannan kuma ya ce, yana nuna farin cikin sa bisa ga yadda yaga dimbin al’ummar musulmin wadanda suka fito daga sassa daban daban na cikin garin Legas suka halarto wannan taro da fatan Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.

Ya cigaba da cewa kuma yana isar da sakonsa na godiya ga dumbin alummar musulmin cikin garin Legas da sauran wadanda Allah ya hore masu abin hannu kuma suke tallafawa wannan kungiya domin ta cigaba da taimakama marayun jihar Legas suma da fatan Allah ya saka masu da alheri da gidajen Aljanna sannan ya kara da cewa babu shakka kungiyar tana cigaba da samun nasarori na gudanar da irin wadannan ayyukan na tallafa wa marayu kuma al’ummar musulmi na jihar Legas suna yin matukar kokari na gudunar da irin wadannan ayyukan na alheri ya kara da cewa haka zalika ya cigaba da cewa ko akwana kwanan nan wani bawan Allah daya bukaci asakaya sunansa ya tallafama wannan kungiya da wani kata faren fili mai yawa wanda kungiyar ta bayar da tallafin ga marayun jihar Legas zata ginama marayun Legas da kunan kwana bangaren maza da mata da azuzuwan koyan karatun boko dana arabiya da wuraren koyan karatun sana hannu suma bangaren maza dana mata karatun safarta kumfuta da gyaran talbishon da rediyo da gyaran kekunan dun ki da walda da dai sauran makaman tansu ya kara da cewa haka zalika bangaren mata suma zaa gina masu azuzuwan koyan karatun kwamfuta da koyan dunkin keke da yin jakun kunan hannu na mata da sauran makaman tansu.

Yace da fatan Allah ya sakama wannan bawan Allah da alheri sauran jawaban da suka gudana awAjan taron walimar wadanda suka fito daga ba kunan alumma da ban da ban wadanda suka samu halartar taron walimar sun kar katane awAjan sanya albarka wAjan muatnen da suka kir kiro ita wannan kungiyar ta bayar da tallafi ga marayu da wadan da suke tallafa mata domin ta cigaba da gudanar da aiyukan Allah sukace da fatan Allah ya saka masu da gidajen aljanna.

Exit mobile version