Kungiyar Buhari Na Kowa Ta Raba Shinkafa Ga Marasa Galihu A Kebbi

Shinkafa

Daga Umar Faruk,

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yaba wa kkungiyar ‘Buhari Na Kowa’ kan alherin da ta yi na bada tallafi ga marayu, zawarawa da masu karamin karfi a Jihar ta Kebbi bisa tsarin taimakon al’ummar  kasa.

Gwamna Bagudu ya bayyana hakan ne a wajen bikin raba kayan shinkafa da hatsi iri daban-daban ga marayu, zawarawa da masu Karamin karfi a matakin kungiyar reshin  Jihar  Kebbi a karkashin jagorancin Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar ta Kebbi, Alhaji Bello DanTani, Argungu.

Gwamnan wanda ya sami wakilcin Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Alhaji Abubakar Chika Ladan, ya ce gwamnatin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta ba da fifiko kan inganta walwalar marasa galihu da marasa karfi a jihar tare da mai da hankali kan marayu da makamantansu da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Ya kuma bayyana cewa rabon hatsin da “kungiyar Buhari Na Kowa’  Kungiyar ta yi daidai da manufofin gwamnati mai ci don daukaka zamantakewar jama’a da tattalin arzikinsu.

Buhu da kari , Gwamnan ya kuma ce tuni gwamnati ta rarraba kayan abinci da suka hada da shinkafa, gero, masara da suga a dukkanin Kananan hukumomi ashirin da daya a matsayin tallafin azumin watan Ramadana.

Shugaban kungiyar ‘Buhari Na Kowa’ a jihar Kebbi, tsohon mataimakin gwamna Alhaji Mohammed Bello Dantani, Magajin Rafin Kabi wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar gudanar da ayyukan ta Jihar Kebbi, ya ce za a rarraba Mota  biyar na hatsin, kuma tuni an sauke kayan, haka kuma   tsakanin mota 30 kuma 40 zasu isa jihar daga baya, don ci gaba da raba wa ga al’ummar jihar.

Wakilin Sakataren Gwamnatin Jihar ta Kebbi, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro ga gwamnan Jihar,  Manjo Garba Rabiu Kamba mai ritaya, ya yaba wa kungiyar kan irin wannan Karamcin wanda ya bayyana a matsayin Karin sauki ga mutanen jihar a wannan lokaci na watan Ramadan.

 

An gudanar da taron bikin rabon kayan tallafin abincin ne a dakin taro na Kwalejin koyon aiki jinya da ke a Brinin-Kebbi a jiya.

Wani malamin addinin Musulunci Sheikh Umar Isa ya yi tunani a kan Umurnin Allah kamar yadda annabi mai daraja Muhammad (SAW) ya kebanta da wajibcin taimakon juna.

Shugaban Darikar Tijjaniyya a jihar Kebbi, Ahmed Usman Mukhtar khalifa a karshe ya yi addu’ar zaman lafiya, tsaro da kawar da talauci a tsakanin al’umma.

Kungiyoyin mutane daban-daban da suka hada da nakasassu, marayu, makafi, makarantun almajirai da masallatai na daga cikin wadanda suka ci gajiyar rabon hatsin na watan Ramadan a Jihar ta Kebbi ta Kungiyar Buhari Na Kowa ta raba wa ga al’ummar a jiya.

 

Exit mobile version