A ranar Juma’a ce, kungiyar ma’abota amfani da yanar gizo suka gudanar da wasu addu’o’I na musamman kan Allah Ya fiddo da daya daga cikin su, Abubakar Idris, wanda aka fi kira da, “Dadiyata” da aka sace daga gidansa da ke Unguwar Barnawa, Kaduna, kwanaki 84 da suka gabata.
Wanda ya shirya taron addu’o’in, Kwamared Yusuf Amoke, ya ce mahalarta addu’o’in duk abokao ne ne da kuma masu fatan alheri ga dan’uwan na su da suka fito daga sassan Jihar.
“Sama da kwanaki 84 kenan da bacewar na “Dadiyata,” mun yi duk abin da muke iya yi, har mun kai ga masu ruwa da tsaki da suka hada da jami’an tsaro, a kan neman jin duriyarsa amma har yanzun babu amsa a kan hakan.
“Muna kuka zukatanmu cike suke da bakin ciki. Dadiyata matashi ne mai kokari ga hazaka, hakanan ta fuskacin Addini da ilimin boko duk ba a bar shi a baya ba.
“Amma abin takaici, ko a wane dalili ne har yanzun sama da kwanki 80 ba mu sami labarin dan’uwan namu ba,” in ji Amoke.
Ya yi roko ga daukacin ‘yan Nijeriya da su sanya shi a cikin addu’o’in su, “Ko Allah Ya sa a dace, dan’uwanmu, abokinmu ya sami dawo wa gida cikin iyalansa.
“Muna neman jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa, domin sanin ko yana raye ne ko a mace.”
Wanda ya jagoranci taron addu’o’in, Malam Mohammed Abdullahi, ya gabatar da addu’o’i ne daga Alkur’ani Mai Girma, na Allah Ya tona asirin wadanda suka sace shi, ta yanda zai sami dawowa cikin iyalansa.
Abdullahi ya kuma yi rokon ga shugabannin kasa ya kuma bukace su da su ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su amfani talakawa.
Hakanan wani dan siyasa, Sir Jalal Falal, ya kwatanta Dadiya da cewa matsahi ne mai kokari, “wanda a kullum fatansa shi ne ganin Nijeriya ta sami ci gaba da bunkasa ga kowane dan Nijeriya.”