• English
  • Business News
Thursday, August 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kungiyar Ma’aikatan AKTH Na Da Burin Kafa Bankin Kanta – Abba Yakasai

by Mustapha Ibrahim
2 years ago
in Rahotonni
0
Kungiyar Ma’aikatan AKTH Na Da Burin Kafa Bankin Kanta – Abba Yakasai
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban kungiyar tsimi da tanadi na ma’aikatan asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), Malam Kabir Abba Yakasai ya bayyana cewa, kungiyar na yunkurin kafa bankin kanta, domin bayar da kananan basuka ga kananan masana’antu da marasa karfi.

A cewarsa, an kafa kungiyar tsimi da tanadi ne a 2002, domin hada kai da taimakon juna na ma’aikatan asibitin koyarwa na Aminu Kano, kuma zuwa yanzu tana da mambobi 1909. Ya ce a shekaru 22 da kungiyar ta yi, mambobinta sun gajiyar wannan gamayya ta tsimi da tanadi na ma’aikatan ta hanyar mallakar gida, fili ko mota da sauransu.

  • Yadda Sakacin Likita Ya Jawo Rubewar Hannun Jariri A Kano

Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma’a da ta gabata a Jihar Kano.

Ya ce idan aka yi la’akari da daruruwan babura da motoci da gidaje da filaye da kayan abinci da wadannan ‘yan kungiya ke amfana da ita, to lalle akwai bukatar duk inda ma’aikata suke na gwamnati ne ko na kamfanoni su yi kokari su kafa irin wannan kungiya domin amfaninta ga ma’aikata.

Ya ce ita dai wannan kungiya ta hadin kai tana samun kudinta ne ta hanyoyi kamar uku da suka hada da daukar kashi goma cikin 100 na riba na abin da kungiyar tasaya wa ma’aikaci ga mai bukata, sai biyan naira 200 ga duk dan kungiyar da kuma ribar hannin jari da aka sa a kungiyar ko aka siyar.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

Shi ma jami’in kididdigar na kungiyar tsimi da tanadi, Malam Abubakar Sadik Sani ya ce abun sha’awa a wannan harkar babu kudin ruwa ko riba a wannan kungiya, komai an tsarawa shi ne daidai na addinin Musulunci, hatta bashin da ake bai wa ‘ya’yan kungiya babu ruwa a cikinsa, don haka wannan tsari yana taimaka wa ma’aikata kwarai da gaske.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Jerin Kasashen Da Ke Fama Da Tsananin Zafin Da Ba A Taba Yi Ba

Next Post

Wane Irin Hadari Amurka Take Son Ta Kawar?

Related

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
Rahotonni

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu

2 weeks ago
Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
Rahotonni

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

2 weeks ago
Fyade
Rahotonni

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

3 weeks ago
APC
Manyan Labarai

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

3 weeks ago
Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Sanar Da Dakatar Da Ayyukanta Saboda Alhinin Rasuwar Buhari
Labarai

Na Shiga Aikin Soja Domin Gujewa Yin Auren Fari Da Ƙuruciya — Buhari

4 weeks ago
Ko Yanzu Tinubu Ya Yi Rawar Gani, Kuma Yana Ƙoƙari Sosai – Buhari
Rahotonni

Muhimman Abubuwa 10 Da Kowa Zai So Ya Sani Game Da Marigayi Shugaban Ƙasa Buhari

4 weeks ago
Next Post
Wane Irin Hadari Amurka Take Son Ta Kawar?

Wane Irin Hadari Amurka Take Son Ta Kawar?

LABARAI MASU NASABA

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

August 7, 2025
Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

August 7, 2025
Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

August 7, 2025
Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

August 7, 2025
Neja

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago

August 7, 2025
Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

August 7, 2025
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

August 7, 2025
Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

August 7, 2025
NAF Ta Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Zamfara

An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara

August 7, 2025
An Bude Gasar Wasannin Ta Duniya Ta 2025 A Chengdu

An Bude Gasar Wasannin Ta Duniya Ta 2025 A Chengdu

August 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.