CRI Hausa" />

Kungiyar Manema Labaru Ta Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoto Kan Aikin Watsa Labarai Na Kasar Sin

Labarai Na Kasar Sin

Kungiyar manema labaru ta kasar Sin a yau Litinin ta fitar da wani rahoto na musamman, inda ta yi bayani kan yadda ake raya aikin watsa labarai a kasar ta Sin.

Rahoton ya fi mai da hankali kan yadda aka yi kokarin raya wasu kafofin watsa labaru na gargajiya irinsu jaridu, da rediyo, da telabijin, gami da yadda aka hada wadannan kafofin da wasu sabbin fasahohi na zamani. Yanzu haka aikin watsa labarai na kasar Sin na samun ci gaba cikin sauri, musamman ma a bangarorin tsarin aiki, da manufofi, da kwararru, da fasahohi, kana kafofin watsa labarai na kokarin yin amfani da fasahohin zamani da suka hada da 5G, da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, da 4K/8K, da dai sauransu, don kyautata ayyukansu.

Rahotanni na cewa, ya zuwa shekarar 2019, yawan masu aikin jarida na kasar Sin ya zarce miliyan 1, wadanda a cikinsu aka fi samun samari da ’yan mata masu digirin karatu na 2 ko na 3. Kana ana kokarin kare hakkinsu a fannin aikin zama dan jarida. (Bello Wang)

 

 

 

Exit mobile version