Musa Muhammad" />

Kungiyar Matasa Ta Nemi A Hada Hannu Don Ci Gaban Kasar Nan

Wata kungiyar matasa mai fafutukar neman ci gaban kasar nan, mai suna ‘The All Nigerian Youths Project (ANYP)’ ta yi kira ga al’ummar kasar nan da a hada karfi da karfe, a sanya kishin kasa wajen ganin kasar nan da al’ummarta sun ci gaba fiye da kowace kasa a duniyar nan.

Wannan kira yana kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Dk Sulaiman Shu’aibu Shinkafi ya sanya wa hannu, kuma ya mika wa wakilinmum a Abuja.

Dk. Shinkafi, wanda yake kuma shi ne mai rike da sarutar Sarkin Shanun Shinkafi, ya kuma yi tsokaci game da halin da ake ciki, inda cutar Kororna ta jefa jama’a cikin mawiyacin hali, wanda wannan yanayi ya taba tattalin arzikin duniya, na gwamnati da na daidaikun jama’a.

Don haka sai ya yi kira ga Hukumomi da sauran masu hannu da shuni da su tallafa wa jama’a marasa karfi, musamman a cikin wannan yanayi da ake ciki, wanda kowa ke ji a jikinsa.

Shugaban matasan ya kuma yi bayani game da dalilan da suka sanya su suke yin kira ga Tsahon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi ya fito domin yin takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2023 mai zuwa, inda ya ce in har Tsohon Sarkin ya amince, to abin zai haifar wa kasar nan da mai ido.

Don haka ya yi kira ga shi Tsohon Sarkin da ya amsa wannan kira nasu, sannan su kuma al’ummar kasar nan, muddin Sarkin ya amsa zai fito, to ba su da wani zabi in ba shi ba.

Daga nan kuma Dk. Shinkafi ya yi kira ga shugabanni da ’ya’yan kungiyoyin Yarabawa na Afenifere da dattawan Yarabawa na ‘Yoruba Council of Elders,’ da ta matasansu, ‘Yoruba United Front’ da dai sauran kungiyoyin Yarabawa kan cewa su kasance sun sanya ci gaban kasa ne a gabansu fiye da komai.

 

 

Exit mobile version