Daga Idris Umar, Zariya
A makon da ya gabata ne hadaddiyar Kungiyar Matasa da Dattijai (Arewa Trusted Youth and Elders Forum of Nigeria), ta karrama Alhaji Shehu Namadi Samaru, sakamakon muhimman ayyuka da kuma taimakawa al’ummar yankinsu da yake yi.
An gudanar da wannan gagarumin biki ne a babban ofishinsa da ke Iya Abubakar na jami’ar Ahmadu Bello Zariya, inda ya samu halartar manya-manyan baki daga bangarori da dama. Kazalika, Shugaban Kungiyar Kwamared Sani Garba a nasa jawabin, ya bayyana muhimman dalilan da suka sanya kungiyar ta yi tattaki don karrama wannan dan tahaliki da kuma sake ba shi kwarin gwiwar ci-gaba da irin wadannan abubuwan alheri da ya sa a gaba na kyautatawa al’ummarsa na cikin gida da waje.
Kwamared din ya ce; “Abu na farko da kungiyar ta fara yin bincike a kai shi ne, yadda Shehu Samaru a koda yaushe ke damuwa da halin da matasa suke ciki tare da tausaya musu matuka da gaske. Haka zalika, ya juma da daura damarar sama wa wadannan matasa guraben karo karatu a makarantu daban-daban don rage zaman banza a tsakanin su a nan gida da waje.
Bayan Kwamared Sani ya mika wa wanda aka karrama, wato Alhaji Shehu Namadi kambun yabon, nan take al’ummar da ke wajen suka shiga fara tofa albarkacin bakinsu. Daga cikin su akwai Malam Kabiru na Allah Karfashe. wannda ya bayyana farin cikinsa da kuma bayyana cewa, ko shakka babu Alhaji Shehu ya cancanci wannan karramawa, kazalika sun ji dadin da kuma godiya ga Allah da ya kawo mu wannan lokaci, don kuwa tabbas ya cancanci yabo a bisa yadda yake gudanar da harkokinsa ga jama’ar da suke tare da shi a duk inda ya sami kansa, don haka mun ji dadi sosai.
Shi ma Kakakin Samaru Alhaji Ali Gosula, ya nuna jin dadinsa tare da jinjina ga Shugaban Kungiyar tare fatan za su ci gaba da zakulo mutane irin su Alhaji Shehu Namadi ,don ba su kwarin gwiwar taimakon al’ummarsu wanda hakan zai sa a sami ci-gaba a kasa baki daya.
A karshen taron wakilinmu ya samu zantawa da wanda aka karramar wato, Alhaji Namadi Shehu, don jin ko ya yaji a kan samun wannan karramawa da aka yi masa?
Alhaji Shehu Namadi ya bayyana jin dadinsa, inda ya ce; “Ko shakka babu, wallahi a yau ina cike da farin ciki matuka kuma babu wani abin da zan ce sai godiya ga Allah madaukakin Sarki, don kuwa shi ne mai ba ni ikon yin komai a lokacin da ya so. Saboda haka ina sake mika godiyata a gare shi, ina kuma mika godiyata ga wannan kungiya mai albarka, Allah Ya saka masu da alherinsa Ya kuma bar zumunci. Haka zalika, zan so na yi amfani da wannan dama don yin kira ga sauran abokaina ‘yan siyasa, da mu kula da abubuwan da suka shafi al’umma, dalili kuma a halin yanzu kiwon mutum ake yi ban a dabba ba. Duk abin da mutum yake yi al’umma na kallon sa, ashe ni ma da abin tsiya nake aikawa, da haka nan wadannan mutane za su bayar da shaida a kaina. Don haka na yi farin ciki kwarai da gaske, Allah Ya saka da alheri Ya kuma mai da kowa gidansa lafiya, amin.