Connect with us

SIYASA

Kungiyar Yakin Neman Zaben Saraki Ta Nada Kakaki

Published

on

Bayani ya nuna cewa, kungiya yakin neman zaben Sanata Abubakar Bukola Saraki (ABSCO) ta zabi Mista Ilemona Onoja a matsayin kakakinta a fafutukan da ake yi na ganin Jami’yyar PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takaranta a zaben 2019, nadin ya fara aiki nan take.

Bayanin da muka samu ya nuna cewa, Mista Onoja, wanda lauya ne, ya yi karatu ne a jami’ar jihar Binuwai daga nan ya wuce Makarantar Lauyoyi ta Legas ‘Nigerian Law School’ harabar majarantar dake Legas, in daga nan ne ya zama kwararrwn lauya a shekarar 2006.
Sanarwa wannan nadin ta fito ne daga hannun shugaba kwamitin yakin neman zabe Saraki, Hon Mohammed Wakil, ya kuma ce a cikin yan shekarun nan, Onoja, na cikin manyan masu da’awar kira ga gudanar da Mulki a cikin adalci da mutuntuta hakkin yan kasa da kuma tabbatar da bin doka da oda.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: