Ƙungiyar ‘Yan ta’adda ta Ansaru mai alaƙa da Kungiyar Al-Qaeda da ke ayyukanta a arewa maso yammacin Najeriya ta yi watsi da zargin da ake mata na hannu a harin da aka kai kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris din 2022.
Kafar yada labari ta BBC ta rawaito cewa, a ƙalla mutum tara ne suka mutu a harin, sannan an sace wasu, wasu kuma suka ɓata.
- Jami’an DSS Sun Cafke Wani Babban Kwamandan ISWAP A Kano
- Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Ansaru ta ƙaryata zargin ne a wani saƙo na bidiyo da ta saki ranar 12 ga watan Yuni a shafukanta na Telegram da RocketChat.
Mai magana a cikin bidiyon ya yi jawabin ne da Larabci sannan ya yi da Hausa.
An ga a ƙalla mutum bakwai a bidiyon dukkansu sanye da takunkumin rufe fuska kuma suna ɗauke da bindigogi.
Mutumin da ke bayanin wanda ba a iya gane shi, ya tsaya a tsakiya ne yana magana kan abin da ya kira “labarin ƙarya da yake yaɗuwa cewa ƙungiyar Ansarul al-Muslimin fi bilad al-Sudan (cikakken sunan ƙungiyar) ta ɗauki alhakin kai harin jirgin ƙasan.”
Ya ƙara da cewa “wannan ƙarya ce tsagwaronta wacce ba ta da tushe.”
Ya ce Ansaru ba ta da hannu ko kaɗan a harin jirgin ko sace fasinjojinsa.
Hukumomi a Nijeriya sun zargi Ansaru, wacce ke ayyukanta a yankin, da kuma ƙungiyar Boko Haram, wacce take da ƙarfi a arewa maso gabas, da hannu a kai wa jirgin ƙasan hari, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar hada kai da ƴan bindigar da suke ayyukansu a yankin.
Ƴan bindigar sun yi ta sakin bidiyo da hotuna na mutanen da aka kama a jirgin tun bayan harin.
Mai magana a madadin Ansaru din ya ce an tsara “labarin ƙaryar” ne don a zubar wa ƙungiyar mutunci, inda ya jaddada cewa tana ƙoƙarin kaucewa cin zarafin ƴan yankin kuma tana taɓa waɗanda suke adawa ko fito na fito da ita ne kawai.
Tun bayan da ta fara ayyukanta a yankin arewa maso yammacin Nijeriya a farko-farkon shekarar 2021, a lokacin da ta bayyana mubaya’arta ga ƙungiyar al-Qaeda, Ansaru ta matsa wajen nesanta kanta da amfani da tsauraran hanyoyin masu ikirarin jihadi kamar su Boko Haram da IS da kuma ayyukan ƴan binciga.
A wani saƙonta na baya-baya, Ansaru ta nanata cewa tana neman hadin kan mutane ne ta hanyar da’awa maimakon yaƙarsu.
Mai maganar ya ce Ansaru ta yi amannar cewa harin jirgin ƙasan ba shi da alaƙa da jihadi kuma yin hakan ma jawo fitina ne kuma ya saɓa wa Musulunci da aƙidar masu jihadi.