Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RAHOTANNI

Kungiyar Yarabawa Ta Tsame Kanta Daga Kiraye-kirayen A Raba Kasa

by Sulaiman Ibrahim
March 30, 2021
in RAHOTANNI
1 min read
Kungiyar Yarabawa Ta Tsame Kanta Daga Kiraye-kirayen A Raba Kasa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mustapha Abdullahi

Shugabannin kungiyar jin dadi da walwalar al’ummar Yarabawan Nijeriya bakidaya dake da babbar hedikwatarsu a garin Ibadan sun fito fili sun tsame kansu a kan kiraye’kirayen da wani ya yi cewa al’ummar Yarbawa su tashi daga Arewacin Nijeriya domin shi zai raba kasa.
Shugaban wannan kungiya, Abdulhakeem Adegoke ne tare da daukacin shugabanni da ya’yan kungiyar na wasa suka tsame kansu da irin wancan kiraye-kirayen a lokacin da suke ganawa da manema labarai a Kaduna.
A taron manema labaran da suka yi a Kaduna sun tabbatarwa da duniya cewa babu wani ko wasu gungun yan siyasa ko masu kokarin tabbatar da son zuciyarsu da za su iya kawo wa Nijeriya cikas domin kawai wata bukata tasu ta biya.
‘Ya’yan kungiyar al’ummar ta Yarbawa sun ce babu ko shakka duk wannan lamari ne da ke tattare da siyasa kawai, ” duk wanda yake da wata nufaka da nufi irin na sisaya ya dace ya san inda zai samu yadda zai cimma burinsa amma ba ta hanyar haifarwa jama’a matsala ba domin kawai ya na neman jama’ar da zai yi siyasa da su”.
Shugabannin sun kuma yi kira ga ‘yan uwa Yarbawa a duk inda suke a fadin Nijeriya da su yi zamansu a inda suke ba tare da matsawa kansu sai sun tashi daga wurin da suke ba, Nijeriya kasa daya ce al’umma daya da ta hada jama’a daban daban har da auratayya tsakanin al’umma Yarbawa, hausawa da Fulani don haka wani can zai zo rana tsaka ya lalata wannan tsarin da duk ci gaban da aka samu, hakika ba zai yuwu ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Sheikh Isma’il Mai Diwani Ya Mika Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Musa Ghana

Next Post

Tinubu Ne Ya Fara Ba Bahaushe Kwamishina A Legas – Dr. Saeed

RelatedPosts

Amin

Yadda Ta Kaya A Taron Tunawa Da Malam Aminu Kano Karo Na 19

by Muhammad
21 mins ago
0

Mun Gamsu Da Yadda Aka Tsara Taron Kan Tsaro Da...

AKCOE

Mataimakin Shugaba Kwalejin AKCOE Ya Zama Jakadan Zaman Lafiya A Nijeriya

by Muhammad
46 mins ago
0

Daga Mustapha Ibrahim, Mataimakin Shugaban Kwalijin Ilimi ta Aminu Kano...

Allah

An Roki Al’umma Su Dogara Ga Allah  

by Muhammad
1 hour ago
0

Daga Yusuf Abdullahi Yakasai, Alhaji Bello Otunba wanda yake daya...

Next Post
Tinubu Ne Ya Fara Ba Bahaushe Kwamishina A Legas – Dr. Saeed

Tinubu Ne Ya Fara Ba Bahaushe Kwamishina A Legas – Dr. Saeed

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version