A ‘yan shekarun nan, wasu ‘yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suna ta yada zancen cewa wai “kasar Sin ta dana wa kasashen Afirka tarkon bashi”. Sai dai wani rahoton bincike na baya-bayan nan da wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Burtaniya, mai suna “Debt Justice”, ta fitar, ya nuna akasin haka.
Binciken, wanda ya shafi kasashe daban daban guda 88, ya nuna cewa, a tsakanin shekarar 2020 zuwa ta 2025, kaso 39% na kudin basussukan waje da kasashe masu karamin karfi suka biya, ya shiga aljihun hukumomi masu ba da lamuni na kasuwanci, kana kaso 34% na kudin ya koma wajen cibiyoyi masu wakiltar moriyar bangarori daban daban, yayin da kaso 13% kacal aka biya cibiyoyi masu ba da lamuni na jama’a da masu zaman kansu na kasar Sin. Dangane da batun, Tim Jones, darektan tsare-tsare a “Debt Justice”, ya ce: “Shugabannin kasashen yammacin duniya suna dora wa kasar Sin alhakin matsalar basussukan da ake bin kasashen Afirka, amma wannan wani mataki ne na karkatar da hankali kawai. Hakika, bankuna, da kamfanoni masu sarrafa kadarori, da masu kula da cinikin man fetur, na kasashen yamma, su ne wadanda ya kamata su dauki mafi yawan alhakin.”
- Ac Milan Na Tattaunawa Da Bayern Leverkusen Akan Yunkurin Daukar Boniface
- Xi Jinping Zai Duba Faretin Sojoji Ta Kan Titin Chang’an A Ranar Uku Ga Watan Satumba Dake Tafe
Rahoton ya nuna cewa galibin masu ba da lamuni a kasashe masu karamin karfi sun fito ne daga kasashen yammacin duniya, kuma kusan dukkansu na son daukar manufa mai tsauri, da kokarin neman mafi yawan riba. Misali, katafaren kamfanin cinikin ma’adinai na Glencore ya dade da kin amincewa da yafewa kasar Chadi duk wani bashi da yake binta. Ban da haka, ko da yake an shafe shekaru hudu da rabi ana tattaunawa, har yanzu Zambia ta kasa cimma wata yarjejeniyar yafe basussuka da wasu masu ba da lamuni masu zaman kansu suke binta, ciki har da bankin Standard Chartered na kasar Burtaniya. A bayyane wannan tsarin basussuka dake nuna taurin kai da kwadayi, da yadda masu ba da lamuni na kasashen yamma ke tsayawa kan karbar kudin ruwa mai yawa, da kuma samun riba cikin gajeren lokaci, su ne ainihin dalilan da ya sa kasashe masu tasowa fadawa cikin mawuyacin hali a fannin biyan bashi.
Sai dai me ya sa har kullum kasashen yamma suke son dora wa kasar Sin laifin “dana tarkon bashi”?
Dalili shi ne, kasar Sin ba ta son zama ‘yar amshin shata ta kasashen yamma. A kullum kasashe masu sukuni na yammacin duniya suna kallon kansu a matsayin masu tsara ka’idoji a duniya, inda suke bukatar kasar Sin da sauran kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa, su bi tsare-tsarensu na ba da bashi. Sai dai kasar Sin tana da ra’ayinta na kanta.
Bayan shiga karni na 21, sai hukumomin kasashen yamma suka fara rage bashin da suke baiwa kasashen Afirka kai tsaye. A nata bangare, kasar Sin ta lura da yanayin da kasashen Afirka suke ciki na fama da koma bayan tattalin arziki, don haka ta gabatar da tsarin samar da rance don taimaka wa kasashen Afirka raya kansu, bisa fasahohin da ta samu a fannin raya kai. Inda a wani bangare kasar Sin ta samar da dimbin bashin da wa’adin biyansu ke da tsawo, wadanda ruwansu ba shi da yawa, ga kasashen Afirka kai tsaye, yayin da a bangare na daban, kasar Sin da kasashen Afirka suke hadin gwiwa a kokarin gina kayayyakin more rayuwa, bisa amfani da rancen da kasar Sin ta samar. Wadannan al’amura sun nuna ra’ayin kasar Sin na kokarin amfanawa kowa yayin da ake hadin gwiwa.
Ban da haka, kasar Sin ta shiga shirin kungiyar G20 na saukaka matakan biyan bashi ga kasashe masu matsala. A sa’i daya, ba ta dauki dabarar kasashen yamma ta rage bashi bisa sanya wa kasashen Afirka wasu sharuda ba. Maimakon haka, Sin ta fi yin amfani da dabarar dakatar da biyan bashi da kudin ruwa dake tattare da bashin, da tabbatar da manufar tsawaita wa’adin biyan bashin ta hanyar shawarwari, wajen taimakawa kasashen da suke da bukata, dabarar da ta yi amfani gami da samar da sakamako mai kyau, yayin da ake kokarin gwada ta.
Kasar Sin tana amfani da dabaru da fasahohin da ta samu a fannin hada-hadar kudi yayin da take raya tattalin arzikinta, wajen taimakawa kasashen Afirka fid da kansu daga wani kangin yawan cin bashi ba tare da samun ci gaban ba, da dogaro kan matakan yafe bashi, domin kyautata dabarun amfani da kudin da aka samu, da inganta tsare-tsaren aiki. Sai dai a ganin kasashen yamma, matakin tamkar wata barazana ce ga babakeren da suka kafa a fannin hada-hadar kudi.
Saboda haka, ‘yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka fara alakanta kasar Sin da matsalar biyan bashi da wasu kasashe masu tasowa ke fuskanta. Sai dai, a hakika, matakin da suka dauka tamkar dai abin da Hausawa ke cewa ne wato “Kura za ta ce da kare maye”. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp