Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ko Kin San?
Wasu daga cikin abubuwan da suke jawowa ma’uarata matsala su ne irin kuskuren da suke yi tun suna sabbin ma’aurata. Wanda suka kasa fahimtar kuskure ne ko kuma sun sani sun bi son ransu.
- Shin Arsenal Ta Barar Da Damarta Ta Lashe Firimiya?
- Shin Arsenal Ta Barar Da Damarta Ta Lashe Firimiya?
Zaman aure tamkar yi wa yaro tarbiyya ne, duk irin tarbiyyar da kai masa da ita zai taso. To haka Zamantakewa rayuwar aure take.
Yadda kuka soma shi tun kuna sabbin ma’aurata da wannan zamanku zai dore, ana samun akasin hakan bayan kun saba da shi ana iya samun matsala.
Ga wasu kurakuren da akasarin sabbin ma’aurata suke yi wadanda kuma suke zame masu matsala daga bisani.
Na daya: Saba wa juna da abin da ba zai dore a. Muddin ma’aurata suka biye wa dokin amarci suka shigo da wata dabi’a ko halin da suka san ba zai dore ba to a gaba ana iya samun matsala.
Misali namiji ya ce duk abin da matarsa ke so zai mata shi a kuma lokacin da take so. Muddin ya saba mata da hakan duk ran da ya kasa yin hakan zai iya fuskantar matsala daga gare ta. Ko kuma ya ce a kullum sai ya shigo mata da wani abinci ko abin sha da take so. Ba kowace mace ba ce take iya yin uzuri da wannan sabon a lokacin da ta ga an kwana biyu ba a yi mata hakan ba.
Wasu ayyukan gida na kyautatawa da ba lallai bane mace ta yi su, irin debo ruwa a famfo ko rijiya, zuwa kasuwa cefene, yi wa miji wanki ko guga, muddin ta san ba za ta dore da aikata irin wadannan ayyukan ba kada ta saba wa miji da yin su. Saboda duk randa aka kwana biyu ba ta yi su ba zai iya zamo musu matsala.
Na biyu: Rashin yi wa juna gyara; Idan ma’aurata suka saba da duk abin da kowa ya yi dai-dai ne, to daga ran da wani ya yi kokarin gyara wa guda kuskurensa za a iya samun matsala.
Dole ku saba bai wa junanku shawara da kuma yi wa juna gyara a wani kuskure tun kuna sabbin ma’aurata. Hakan zai sa gaba wani ba zai ga abin a matsayin raini ko kiyayya ya sa da ba a yi amma yanzu an tsiro yi.
Na Uku: Ci gaba da soyewa kafin Aure:
Soyayya kafin aure da kuma soyayya bayan aure suna da bambamci. Soyayya kafin aure masoya na iya fita yawon shakatawa duk inda suke son shiga. Soyayya bayan aure dole ma’aurata su yi la’akari da wurin da za su shiga. Masoya suna iya fita yawo a duk lokacin da suka tsara. Soyayya bayan aure hakan zai iya samuwa ne kadai a lokaci zuwa lokaci saboda matsaloli na rayuwar aure.
A soyayya kafin aure duk wasu bukatu na masoya su kan yi kokarin biya wa juna. Soyayya bayan aure bukatun da suka zama dole kuma masu mahimmanci su ake kulawa. Duk zuwa wajen mace a lokacin soyayya kafin aure sai saurayi ya je mata da wani abin kwalama ko kuma ya mata kyauta musamman ga mazan da ba kullum suke zuwa ba. Amma shi soyayya bayan aure wani lokacin ma miji zai dau lokaci ba tare da yana da abin da zai kawo gidan nasa na dole bare kuma na kyauta.
Ire iren wadannan abubuwan dole ne sabbin ma’aurata su saka a ransu ba irin soyayar da suka yi kafin aure ba za su yi bayan aure ba. Hakan kuma ba yana nufin ba sa son junansu ba, sai dai yanzu zama ne na har abada dole ne su rika yin abin da za su iya ci gaba da yin sa.
Na Hudu: Samun ‘Yanci; Daga lokacin da sabbin ma’aurata suka bai wa kansu ‘yancin yin abin da suke so a lokacin da suke so, gaba zai iya zame masu matsala idan suka yi kokarin neman gyarawa.
Kada ango ya ce zai bar matarsa ta yi abin da take so, ta je inda take so a lokacin da take so. Ko ta shiga irin yadda ta ga dama. Idan ya kau da kai a yanzu saboda soyayya to gaba zai iya yin wuya ya ce zai gyara lamarin ba a samu matsala ba.
Haka itama mace kada ta kau da kai ta bar mijinta yana yin abin da ba kan ka’ida ba saboda tunanin yanzu suka yi aure.
Fita hiran banza majalisa tun kuna sabbin ma’aurata za ki nuna masa baki so. Dawowa gida lokacin da mijinki ya ga dama ba tare da hujja abin kamawa ba yanzu za ki takawa hakan birki. Hira da wasu matan a waya a gabanki kada ki bari ya saba tun yanzu. Cin fuska ko zagi tun kuna sabbin ma’aurata za ki hana shi idan kin fahimci yana neman shigo da su.
Na Biyar: Jima’i; Idan ma’auratan nan yanzu suka taba aure, to kada su sabawa kawunansu yin Jima’i da nan gaba zai iya cutar da su. Kada ya zama sabon ku da Jima’i a lokacin amarci zai iya takura guda daga cikinku idan hakan bai samu ba a lokacin da ake bukata. Don haka ku sabawa juna abin da za ku iya ko da nan gaba an samu lalura na rashin lafiya ko kuma tafiya.
Wadannan dama wasu dalilan birjib sune wasu daga cikin kurakuren da sabbin ma’aurata suke yi wanda daga karshe hakan na shafar Zamantakewar aurensu. Da fatan za a kiyaye. Allah Ya ba da zaman lafiya.