Wani Shahararren Malamin addinin musulunci mai akidar bin Alkur’ani zalla da ke zaune a jihar Katsina, Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka ya warware fatawar da wani malami da su ke akida daya a jihar Kaduna yayi na cewa “cin naman kare ba haramun bane a karantarwar Alkur’ani”.
Malamin na Kaduna ya yi da’awar cewa, acikin Alkur’ani gaba daya babu wani wuri da aka hana cin naman Kare, sabida haka ya yanka Kare a makarantarsa kuma ya raba naman ga Dalibansa da wasu mutane a unguwarsa.
Al’amarin da ya jawo cece-kuce a tsakanin al’ummar musulmi a jihar dama wasu jihohin kasar nan.
An rahoto cewa, al’amarin ya sanya wasu fusatattun Matasa rushe gidan malamin sakamakon wannan sabuwar da’awa.
Sai dai, Sheikh Masussuka da ya ke zantawa da wakilin LEADERSHIP Hausa, ya warware fatawar wancan malamin na Kaduna da yayi ikirarin shi mmabiyin Alkur’ani ne zalla, inda yace waccar fatawar ba koyarwarsu bace.
Masussuka yayi nuni da cewa, a Alkur’ani Allah ya ambata amfanin Kare da yin gadi ko farauta kamar yadda ya ambata doki, jaki da alfadari a matsayin ababen hawa.
Yace tunda Allah ya riga ya fadi amfanin kare da yin gadi da farauta, ba bukatar a fada wa mutum cewa “ba a ci” domin da ana ci, “Alkur’ani zai fada kamar yadda ya halatta cin sauran dabbobi irin su raguna, awaki, shanu da sauransu”.
Sabida haka, Masussuka yace, wancan malamin da ake cewa dan Kur’aniyyun ne bai fahimci Alkur’ani ba.