Yanzu haka halin rashin tabbacin da duniya ke ciki yana kara tabarbarewa, kuma farfadowar tattalin arzikin duniya ya yi rauni. Ina duniya ta dosa? Kasashen BRICS za su ba da amsarsu. Yayin da taron kolin BRICS na shekarar 2024 ke gabatowa, wani bincike da kafar CGTN ta gudanar kan masu amfani da yanar gizo na duniya ya nuna cewa, mafi yawan wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu na fatan hadin gwiwa na BRICS zai kara kuzari ga tattalin arzikin duniya da ke tangal-tangal, da daidaita tsarin harkokin duniya mai sarkakiya.
A cikin binciken, kashi 92.87 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, wannan tsari yana sa kaimi ga yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Kuma kashi 94.2 cikin dari na ganin cewa tasirin tsarin hadin gwiwa na BRICS yana ci gaba da fadada, kana kashi 94.1 cikin dari sun bayyana cewa, a matsayin tsarin hadin gwiwar bangarori daban-daban da ya kunshi kasashe masu tasowa, kasashen BRICS na iya kara kuzari ga farfadowar tattalin arzikin duniya.
Binciken wanda aka wallafa a kafar CGTN cikin harsunan Turanci, Sifaniyanci, Larabci, Faransanci, da Rashanci, a cikin sa’o’i 24, ya samu jimillar masu amfani da yanar gizo da suka bayyana ra’ayoyinsu 18,961 daga kasashe daban daban. (Yahaya)