“Shugabar Japan ta furta kalamai da ba su dace a ji su ba, ta kuma tsallaka jan-layi da sam bai dace a taba ba”. Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a na kafar CGTN, ya nuna yadda masu bayyana ra’ayoyi suka fahimci, tare da nuna goyon bayan aniyar kasar Sin na sukar matakan tayar da zaune-tsaye na firaministar Japan.
Sakamakon kuri’un jin ra’ayin sun nuna yadda kaso 86.2 bisa dari na masu bayyana mahanga ke ganin manufar kasar Sin daya tak a duniya ta kafu, kuma ta samu amincewar bai daya tsakanin sassan kasa da kasa. Kazalika, kaso 90.7 bisa dari sun amince cewa Japan a matsayinta na wadda ta sha kaye, wajibi ne ta ci gaba da martaba ka’idojin da kasashen duniya suka gindaya. Yayin da karo 93.9 bisa dari ke kira ga gwamnatin Japan din ta zurfafa tunani game da halayyarta, ta mulkin mallaka kan yankin Taiwan, da laifukan yaki ta amfani da karfin soji, kana ta yi taka-tsantsan, da kiro da matakai da aka tabbatar dangane da batun Taiwan da na tarihi.
Kafar CGTN ta wallafa kuri’un jin ra’ayoyin ne da harsunan turancin Ingilishi, da Sifaniyanci da Faransanci, da Larabci da harshen Rasha. Kuma masu bayyana ra’ayoyi 7,740 sun fayyace mahangarsu cikin sa’o’i 12. (Saminu Alhassan)














