Wani mai goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Celtic, ya afka cikin filin wasa da zimmar kai hari kan dan wasan PSG Kylian Mbappe a yayin fafatawar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Talata a gasar zakarun kungiyoyin Turai.
Lamarin ya faru ne a lokacin hutun rabin lokaci a filin wasa na Celtic Park, wato jim kadan ke nan da kwallo ta uku ta PSG ta zura a ragar Celtic.
Celtic wadda ta karbi bakwancin PSG, za ta fuskanci hukunci daga hukumar kwallon kafar nahiyar Turai.
Kocin Celtic, Brenden Rodgers, ya ce, kungiyar za ta hukunta wannan mutumin da ya aikata wannan laifi na kokarin kai hari kan Mbappe da ya zura kwallo ta uku a fafatawar da suka yi nasara da ci 5-0.
A karon farko ke nan da Celtic da ta kasance zakara a Scotland, ke shan mummunan kashi a gida a wata gasa a nahiyar Turai.