- Har Yanzu Galibin Mutane Ba Su Fahimci Muhimmancinsa Ba
- AkwaiKarancin Ma’aikata
- Wasu Makota Na Yi Masa Zagon Kasa
- ‘Yan Sumoga Sun Addabi Harabarsa, In Ji Daraktansa
LEADERSHIP HAUSA ta yi tattaki zuwa Asibitin Kutare na Bela da ke kan hanyar Gezawa a karamar hukumar Tofa ta Jihar Kano, domin kawo wa masu karatunmu labari a kan halin da asibitin ke ciki, da kuma fahimtar da al’umma irin ayyukan kiwon lafiyar da yake yi domin ‘yan kasa su ci gajiyar asibitin.
Wakilinmu SABO AHMAD KAFIN-MAIYAKI ya zanta da Daraktan Shiyya na hukumar da ke kula da asibitocin Jihar Kano, shiyya ta daya, wadanda suka kunshi Asibitin Kutare na Bela, da Asibitin Zana da na Hakori, ABDULLAHI ISMA’ILA KWALWA. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:
Darakta, barka da warhaka. Masu karatunmu za su so, ka gabatar da kanka.
Sunana Abdullahi Isma’ila Kwalwa. Ni ne Daraktan shiyya na hukumar da ke kula da asibitici a jihar Kano, shiyya ta daya da ke kula da Asibitin kutare na Bela da Asibitin Zana da Asibitin Hakori da kuma wasu asibiti guda uku kanana, wadanda suke kunshi asibitocin shiyyar guda shida.
Menene tarihin wannan asibitin kutare na Bela?
An kafa wannan asibiti a shekara ta 1930, lokacin Sarkin Kano, Abdullahi Bayero. An yi niyyar kafa wannan asibitin ne da a garin Sumaila, amma sai aka zo aka yi shi a wannan muhallin da kake ganinsa a halin yanzu, ganin cewa, a wannan gurin zai fi saukin shiga da fita, musamman ga wadanda ke nesa, amma saboda yanayin irin mutane da ke jiyya a wannan asibiti, ya zama an nesanta shi daga cikin al’ummar gari, yadda majiyayyata za su samu walwala ba tare da nuna tsangwama ba daga wasu al’umma. Asibitin Bela asibiti ne da ke da haraba mai fadin gaske. An debi wannan harabar ce, tun a wancan lokacin bisa hasashen duk loacin da aka bukaci fadada shi, za iya fadada shi ba tare da wata matsala ba.
A cikin shekara ta 1975, Gwamnan Jihar Kano Audu Bako a wancan lokacin ya zo ya yanki wani bangare na wannan asibiti, ya sa aka haka dam. Sai dai babban abin takaici shi ne, yadda wasu bata-gari ke neman hana ruwa gudu a wannan asibiti, musamman wasu daga cikin makotan asibitin, ta hanyar karkatar da wasu marasa lafiya zuwa wasu a sibitoci masu zaman kansu, wanda hakan na daga cikin abin da ya zame wan nan asibiti alakakai.
Tun daga wancan lokacin zuwa yanzu, asibitin ya kai kusan kimanin shekara dari da kafa shi, saboda haka, yana da dogon tarihi, tun lokacin Turawan milkin mallaka.
Tun daga wancan lokacin da aka kafa shi, ya ci gaba da samun ci gaba, inda bayan kasancewarsa asibitin kutare ya zama ana karbar haihuwa a cikinsa, an kuma samu dakin gwaje-gwaje da kuma dakin daukar hoto, samar da wadannan ayyuka da ake yi a wannan asibiti, sai aka daga darajarsa ya tashi daga asibitin kutare, ya zama Babban Asibiti. Saboda haka sai ya zama yana samar da lafiya ga yara da mata da sannan kuma ana kwanciya a cikinsa, sannan kuma asibitin na yin ayyukan riga-kafi.
Saboda haka ida aka dubi asibitin a halin yanzu za a iya cewa, ya samu ci gaban da majiyyata ke zuwa daga kowane sashi na kasar nan domin a kula da lafiyarsu, kuma daidai gwarwado suna samun biyan bukata.
Wadanne kakubale wannan asibiti ke fuskanta a halin yanzu?
Babban kalubalen da wannan asibiti ke fuskanta shi ne, karancin ma’aikata, a wannan asibitin muna da bangaren sha-ka-tafi, muna da kwararrun likitoci a bangaren fata, saboda haka, dukkan wani likita da zai tura majiyyaci kan aikin fata asibitin Bela zai tura, saboda muna da kwararrun lilitocin fata, a wannan asibitin, wanda ya sa al’umma daga ko’ina da suke da matsalar da ta shafi fata ke zuwa wannan asibitin.
Wannan ta sa nake ganin indai za a yi maganar babban kalubalen da wannan asibitin ke fuskanta bai wuce na rashin wadatattun ma’aikata ba.
Wani babban kalubale, ko kuma in ce babbar barazar da wannan asibitin ke fuskanta ita ce, har yau mutanen da ke makotaka da wannan asibiti ba su fahimci amfaninsa ba. Kusan shekara dari da kafa wannan asibitin amma har yanzu wasu da yawa daga cikin mutanen wajen ba su fahimci muhimmancin asibitin ba, musamman kan yadda za su bayar da gudummowa wajen ganin ya samu ci gaba, saboda haka ka da su dauka cewa, lallai sai gwamnati ce za ta taimaka wa wannan asibitin al’umma sun a suna da gudummowar da za su bayar.
Wata babbar matsala da wannan asibitin ke fuskanta daga wasu mazauna wannan yanki, shi ne yadda sukan bi sawun mara lafiya, yadda za su kwadaitar da shi ya bar wannan asibitin zuwa wani asibitin mai zaman kansa, yadda za su hada baki inda suka kai shi domin su sanu kudi, daga mara lafiya da kuma asibitin da suka kai majiyyaci.
Karin wani babban kalubalen da wannan asibitin ke fuskanta shi ne na tsaro, yadda wasu masu somoga da sauran wasu masu laifi kan keto ta harabar wannan asibiti, wanda hakan ke zaman wata babbar barazana ga wannan asibitin da kuma majiyyatan da ke cikinsa, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar matsalar tsaro, kuma da ma wasu majiyyatan za ka samu baki ne, ba su san yanayin yankin ba, ka ga hakan na iya dagula musu lissafi ta hanyar jefa musu tsoro cikin zukatansu. Shi majiyyaci kullum ana bukatar ya samu kwanciyar hankali ba tashin hankali ba, domin fadawarsa cikin tashin ba zai taimaka masa ba wajen samun lafiyar da ya zo nema ba.
Wane sako kake da shi ga majiyyata da ke wannan Asibiti?
A gaskiya, majiyyata na kokari matuka, ka ga majiyyata kan zo daga nesa, kamar Nijar da Yobe da Maiduguri, kai kusan ko’ina a fadin kasar nan domin neman lafiya, kuma sukan zo ba tare da cewa, sun san wani a wannan gari ba, maganar neman lafiyar ce kawai ke kawo su.
Sai dai babban kiran da zan yi musu shi ne, su kara hakuri, yayin da suka zo wajen neman lafiya, kuma su daure su bi dokokin da likita ya kafa musu, domin su samu warakar da suka zo nema, sannan kuma su yi hankali da wasu mutane da ka iya zuwa wajensu, da niyyar cewa, za su taimake su, su kai su wani asibitin da za a kula da su, cikin gaggawa.
Akwai wani sako da kake da shi musamman ga masu hannu da shuni da ke kusa da kuma na nesa da wannan asibitin?
Babban sakona shi ne, musamman ga masu hannu da shuni, shi ne su yi amfani da damar da Allah ya ba su wajen taimaka wa wannan asibiti wanda dimbin al’umma ke amfana da shi. Domin kuwa da irin wannan gudummowarce wasu asibitoci suka bunkasa, bas a jiran gwamnati, musamman a wannan kasa idan muka lura, za a iya cewa, nauyi ya yi wa gwamnati yawa, saboda haka, akwai bukatar masu hannu da shuni su shiga sahun masu bayar da taimako ga wannan asibiti, mai dimbin tarihin da ya shafe kusan sheka dari yana gudanar da ayyukan lafiya.
Wane sako kake da shi ga al’ummar wannan yanki da wannan asibiti ke ciki, sakona shi ne su kara jin tsoron Allah, su tabbatar sun bayar da gudummowar gina wannan asibitin ba rusa shi ba, wannan kuma zai raimaka wajen su kansu mazauana yankin su kara samun ci gaba.
Ga gwamnati kuma, za mu iya cewa, kokarin da take wajen inganta wannan asibi na taimaka wa majiyyata wajen samun kulawar da ta kamata ga marasa lafiyar da suka zo nema daga mesa da kusa a dukkan fadin kasar nan.