Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kuskuren da shugabannin baya suka yi ne ya jefa kasar nan ciki tasku.
Dan takarar ya bayyana haka ne a birnin Landan, ya yi da ya halarci tattaunawa da ‘yan siyasa da Chatnam House ke yi.
- Rundunar ‘Yansanda Ta Ba Iyalan Jami’anta Da Suka Mutu Da Wadanda Suka Jikkata Biliyan 13
- Cutar Shakewar Numfashi Ta Kashe Mutum 25 A Jihar Kano
“Akwai matsaloli da dama da Nijeriya ke ciki, amma a ganina shugabannin baya ne suka haifar da su.
“Akwai rashin aikin yi, babu ilimi mai inganci, rashawa, rashin kyawun kayan aikin lafiya.
“Idan na samu dama zan gyara wadannan kurakuran da shugabannin suka yi saboda na gano inda gizo ke sakar.”
Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa ta NNPP da magoya bayanta sun shirya tsaf don yi wa Nijeriya sabon tsari da kowa zai ci moriyar dimokuradiyya.
Sai dai dan takarar ya yi karin haske kan yadda hadewar jam’iyyarsa da jam’iyyar LP ta ci tura.
“Abubuwa sun faru a baya kuka tafiyar ba ta yi kyau ba, ita jam’iyyar LP da farko ta fari kamar gishiri da afkinta amma yanzu shiru kake ji tamkar wadda ruwa ya shanye.”
Dan takarar ya alakanta halin da ake ciki da rashin shugabanci nagari wanda aka samu a shekaru 24 da suka wuce a baya.