Daga El-Zaharadeen Umar,
Kwalejin kiwon lafiya ta “Khuddam School of Health Technology’ da ke Katsina ta yi bikin daukar sabbin dalibai a fannoni daban daban da suka shafi harkar kiwon lafiya na gurbin karatu na shekarar 2020/2012 a harabar makarantar da ke Katsina
Taron wanda irinsa ne na farko, ya samu tagomashi daga masana da malamai da kuma masu ruwa da tsaki akan harkokin kiwon lafiya a cikin da wajan jihar Katsina, musamman kasidun da aka gabatar da suke kara zaburar da daliban ilimi akan sha’anin kiwon lafiya.
Hon. Hussain Damba wanda ya ce harkar kiwon lafiya tana cikin wani halin ni ‘ya sa, wanda kuma kafa wannan Kwaleji ta ‘Khuddam School of Healt Technology’ ta zo akan daidai musamman a wannan lokacin da ake da karanci ire-irensu.
“Ina ganin idan aka cigaba da samun makarantun irin wadannan ko shakka babu matsalar da ake fuskanta a bangarorin kiwon lafiya za a samu sauki so sai, ta hanyar samar da sabbin jami’an kiwon lafiya wanda daman ana da karancinsu a wannan jiha da kuma kasa baki daya” inji shi
Shima a nashi jawabin tsohon shugaban hukumar PTDF Injiniya Muttaka Rabe Darma ya nuna mahimmacin samun irin wadanda makarantu a jihar Katsina inda ya ce akwai kalubale so sai a wannan fannin na kiwon lafiya wanda ke butakar kwararun jami’an kiwon lafiya.
Injiya Muttaka Rabe wanda ya gabatar da wata kasida a cikin harshen turanci ta tabo batun yawaitar mutuwar Mata a lokacin haihuwa da su kansu yaran da ake haihuwa wanda ya ce a duniya Najeriya ita ce ta uku.
“Baban abinda yasa ake samun ire-iren wadannan matsaloli na mutuwar mata a lokacin haihuwa baya rasa nasaba da rashin wadatatun jami’an kiwon lafiya wanda idan muka duba kowane fanni sun yi kadan, saboda haka ana bukatar kari so sai ta yadda za a cike wannan baban gebi da ake da shi a kasa da kuma jihar Katsina” inji shi.
Haka kuma ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta kafa wata hukuma da zata rika kula da makarantu irin su ‘Khuddam School of Healt Technology’ domin ganin an samar da jami’an kiwon lafiya kwararu a fadin jihar Katsina.
Kazalika ya yi nuna da cewa idan har gwamnati tasa idon to ba za a kaucewa tsare-tsaran gwamnatin ba, sannan kuma a rika tallafi masu idan butakar hakan ta ta so domin kadda su ruguje da wuri, su kuma dabilai ya ce ya kamata su san abinda ya kawo su wannan makaranta su dage so sai.
Wadanda suka samu halarta wannan biki sun hada da dan majalisar dokokin mai wakiltar karamar hukumar Katsina Honarabule Ali Abu Albaba da Mai taimakawa gwamna akan dawo da martabar jihar da sauran masu ruwa da tsaki akan sha’anin kiwon lafiya da dalibai da dai sauransu.