Connect with us

LABARAI

Kwamandan NDLEA Na Kano Ya Fasa Kwan Masu Sojan Gona Da Sunan Hukumar

Published

on

Ranar 26 ga wata Yuni ne ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta Ware amatsayin ranar da ake gudanar da bikin duba nasarori da kuma irin matsalolin da ake fuskanta dangane da harkar yaki da sha tare da fatauncin miyagun kwayoyi. A jihar Kano Kamar kowace shekara Rundunar Hukumar Kakarshin babban kwamanda Alhaji Hamza Umar ta gudanar da wannan taro a shelkwatar Hukumar dake Kano
Taron na bana wanda aka yi wa lakabi da Ka fara sauraro ya gudana kamar yadda aka saba, Kwamandan Hukumar NDLEA reshen Jihar Kano da yake gabatar da jawabinsa ya bayyana cewa ana gudanar da irin biki a fadin duniya wadda ofishin dake kula da harkokin shaye shaye da kuma manyan laifuka na majalisar dinkin duniya kan shirya inda akanyi nazari tare da bayyana irin hadarin dake tattare da da amfani da miyagun kwayoyi.
Ya ce taron na bana wanda a bisa al’ada mutane daga bangarori daban daban kan hadu domin ilimantar da juna kan batun tattalin arziki, illolin da matsalar shaye shaye kan haifarwa da dai-dai kun matane, rukunin al’umma, kungiyoyi, kasa da ma Duniya baki daya. Ya ci gaba da cewa a kowace shekara akan samar da wani take wanda ke karfafa yaki da shan miyagun Kwayoyi wanda ake fatan jama’a su fara yin la’akari da ingantanciyyar lafiya ba shan miyagun kwayoyi da ake fatan jama’a su fara sauraro.
Alhaji Hamza Umar ya ce zai yi amfani da wannan dama domin bayyanawa al’ummar Jihar Kano dama kasa baki daya irin nasarorin da muka samu daga 26 g wata Jane na shekarar data gabata zuwa yau. Ya ce mun samu nasarar Kame jimlar kayan maye nau’i daban daban wanda suka kai Kilo gram 7,061.582 KG
Haka kuma Alhaji Hamza ya bayyana amincewar da gwamnatin Kano ta yi na gina cibiyar kyautata halayyar mutane da ake sa ran ginawa ashelkwatar hukumar da ke Kano da kuma Karamar Hukumar Kiru wanda ake sa ran ajiye maza da mata.
Hakazalika Alhaji Hamza ya ce yana da kyau Jama’a su san irin gudunmawar da mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhamadu Sanusi IIbbisa kyakkyawan misali da masarautar Kano ke bayarwa, musamman yadda masarautar Kano ta kafa dokar cewa ba wanda za a kara nadawa wata sarauta face an tabbatar da gwajin kwakwalwarsa. Ya kuma jinjinawa Gwamnati bisa kara bude rassan hukumar biyu kari kan guda biyar da ake dasu a kananan Hukumomin Danbatta da Gwarzo, ya ce wannan duk yana daga cikin kokarin shugabannin Kananan Hukumomi, Hakimai da kuma sauran al’ummar dake wadannan yankuna.
Alhaji Umar Hamza ya kuma bayyana sunayen wasu mutane biyar dake yin sojan gona da sunan ma’aikatan Hukumar NDLEA, wadanda suka hada Sabi’i Abubakar, Alhaji Bala Mustapha, Murtala Usman, Malam Ya’u da kuma Musa Haruna Mohammad. Ya ce guda daga cikinsu an taba kama shi shekara biyu da suka gabata ya samu tsallakewa ta fuskan beli wanda yanzu kuma ya kara shiga hannun wannan Hukuma. Ya ce a kokarin da hukumar mu keyi har sai da jami’in mu Tanko Amfani (SAN) ya gamu da ajalinsa ya yinda sauran abokan aikinsa suka gamu da munanan raunuka wanda wasu manyan dillalan kayan maye a Karamar
Hukumar Kiru suka afkawa. Haka kuma a ka kaiwa shiyyar mu dake Bichi irin wannan hari tare da jikkata 2ic wanda aka kusa hallaka shi har yanzu yana nan ya karbar maganai. Shima Wiliiams ya gamu da irin wannan farkamki wanda aka jikkata a Sabon Gari ya yin da yake gudanar aiki amma an samu nasarar damke maharan.
Akarshe Alhai Hamza Umar ya bukaci al’umma su ci gaba da sa ido kan harkokin shaye shaye ta hanyar kafa kungiyoyin sa kai, ya kuma hori jama’a dasu ci gaba bayar da bayanan sirri ga jami’an Hukumar NDLEA, Jama’a su ci gaba tona asirin duk wani sjona gona da ke amfani da sunan jami’in Hukumar NDLEA, sannan ya bukaci iyaye dasu ja hankali yarnsu wajen nusar dasu illar mu’amilla da kayan maye.
Ya ce duk wadannan nasarori basu samu ba sai da hadin kan gwamnatin Kano, fadar mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II CON, haka kuma ina mika godiyar mu ga sauran jami’an tsaro bisa gudunmawar da suke bamu, sai kuma ‘yan jaridu wanda suke sahun gaba a wannan yaki.

Advertisement

labarai