Mustapha Abdullahi" />

Kwamishina Ya Ceto Rayuwar Wani Yaro A Katsina

Kwamishina

Kwamishinan ma’aikatar kula da muhalli ta Jihar Katsina, Honarabul Hamza Sule Faskari ya samu nasarar ceto rayuwar wani bawan Allah da ke fama da karaya a kashin bayansa.

 

Shi dai yaron, kamar yadda muka samu labari yana zauna ne a cikin garin Funtuwa a Unguwar tsohuwar kasuwa.Sai wani daga cikin hadiman Kwamishinan ya zo ya gaya masa irin halin da yaron yake ciki na matsalar samun karaya a tsakiyar kashin bayansa, wanda sanadiyyar hakan wani asibiti ya tabbatar masu da cewa za a yi wa yaron aiki domin a gyara masa kashin, amma sai iyayen sun kawo kudi Naira Miliyan 1,150,000 sannan za a iya yi masa aikin.

 

Cikin hukuncin Allah nan take Kwamishina Hanza Sule Faskari ya ce a kai shi, kuma a halin yanzu har an gama maganar, yaron na can asibiti, sai aiki kawai domin maganar kudi an rigaya an gama ,sai fatan Allah ya ba yaro lafiya da tsawancin kwana.

(woman wityh baby pic)

Exit mobile version