Kwamishinan Muhalli Na Jihar Katsina Ya Tallafa Wa Mutum 3,104 Da Kudade

Daga Abdullahi Sheme

A ranar Asabar din da ta gabatane 17 ga Afirilu 2021 Kwamishinan Muhalli na jahar katsina, Alhaji Hamza Sule Wamban Faskari ya tallafama mutum 3104 da kudade Naira milyan 23 domin sayen kayan Azumi a cikin wannan watan mai albarka a sakatariyar karamar hukumar faskari da ke jihar Katsina.
Tun a farko, a nasa jawabin maraba da baki, shugaban riko na karamar hukumar faskari Alhaji Lawal Danmummuni ya fara da gode wa Wamban na faskari ne Alhaji Hamza Sule, yana mai cewa babu shakka a matsayinshi na Shugaban riko na wannan karamar hukumar bai iya shaida ko sau nawa ya ga yawan taimakon da wannan bawan Allah ya yi ba, domin ya kai shekaru da yawa a wannan karamar hukumar a matsayin Shugaban riko na karamar hukumar babu wani wata da zaizo ya wuce Kwamishinan bai zo ba ko ya aiko da kayan arziki ga al’ummar wannan yanki ba, in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, ba karamin abin Alheri ba ne wannan abin a yaba wa maigirma Kwamishinan ne , da fatar Allah ya saka masa da mafi alheri a dukkan rayuwarsa yana mai rokawa. Ya ci g aba da cewa, babu shakka jama’ar Faskari sun yi sa’a domin ba wata karamar hukumar da tayi dace kamar ku wajen samun mutum mai tausayi da taimakon al’umma kuma murya daya ce a jam’iyar APC a karamar hukumar faskari.
A lokacin da ya ke gabatar da yawan kananan hukumomin da za su amfana da tallafin, Alhaji Bala Ado Faskari tsohon Shugaban matasan jam’iyar APC ta jahar Katsina kuma tsohon Shugaban riko na karamar hukumar Faskari mai jiran gado ya bayyana cewar, kananan hukumomi 5 ne zasu amfana da kudin; wanda su ka hada da: Faskari, Kankara, Sabuwa, Dandume da Funtuwa. A KASAFIN kudaden, akwai wadanda za su karbi 5,000, wasu 10,000 har zuwa kan wadanda za su karbi 20,000.
Jimillar kudin dai baki daya da za a tallafa wa kananan hukumomin 5 da aka lissafa milyan 23, kuma babu wanda zai koma gida ba tare da kudinshi a aljihunshi ba, in ji sa. Ya ci gaba cewa, a gaskiya su dai karamar hukumar Faskari basu taba samun da kamar maigirma Kwamishinan Muhalli Alhaji Hamza Sule ba wajen tausayi da taimakon al’umma ta kowanne hali, da sauran ma makwaftan kananan hukumomin dake kusa da karamar hukumar ta Faskari.
Haka kuma, ya yi kira ga uwar gidan matar maigirma Gwamnan jihar Katsina, Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari Dallatun Katsina, da ta Kara mika godiyarsu ga maigirma Gwamnan a kan yadda yaba dansu mukami a wannan Gwamnati Mai albarka da daya tamkar da dubu, har wala yau ya kara kira ga maigirma Gwamnan jihar da yakara taimakon karamar hukumar don kara samun tsaro a yankin dama sauran kananan hukumomin da suke fama da rashin tsaro koda yake a ‘yan kwanakin nan ansami sauki a cewar sa, dafatan Gwamnatocin guda biyu zasu kara kaimi don kawo karshen wannan ta’addancin da ke janyo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da fatan Allah yajikan wadanda suka rasu kuma ya maidama wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu da alkhairi amin, yana mai rokawa.
Duk a taron, tsohon shugaban riko na karamar hukumar ya cigaba da cewa, mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jIhar, Alhaji Shehu Dalhatu Tafoki shima zai tallafawa mata guda 250 daga wannan karamar hukumar tamu ta faskari da tallafin kudi Naira 5000 ga kowacce mace daga mazabu 10 da ke karamar hukumar, sannan ya yi alkawari duk bayan watanni 3 zai cigaba da tallafama mata 250 don su dogara da kawunansu wajen gudanar da sana’oin hannu a gidajensu, dalilin da ya sa a ka gayyato uwargidan matar maigirma Gwamnan Hajiya Hadiza Mama domin ta shaida wannan abin arzikin kuma cikin wata mai albarka, in ji shi. Babu shakka, al’ummar karamar hukumar faskari muna godiya kwarai ga wannan Gwamnati ta Dallatun Katsina kuma matawallen Hausa.

Exit mobile version