Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya yi kira ga masu ruwa da tsaki daga shiyyar arewa ta tsakiya da su gaggauta fitar da sabon shugaban jam’iyyar na kasa domin maye gurbin Sanata Iyorchia Ayu.
An cimma matsayar ne a taron da ya gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja a wani gagarumin yunkuri na mayar da babbar jam’iyyar adawa ta koma kan turba.
- An Samu Rarrabuwa Kan Yunƙurin Barin Damagum A Matsayin Shugaban PDP Har Zuwa 2025
- ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP
Wannan kudiri wanda yana cikin jerin umarnin da aka fitar yayin wani taron gaggawa ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan halin da jam’iyyar ke ciki.
Da yake karanta sanarwar, shugaban kwamitin amintattun PDP, Sanata Adolphus Wabara ya bayyana matukar damuwarsa kan shugabannin jam’iyyar na rigingimun cikin gida da ake fama da su, da kuma jinkirin warware muhimman batutuwan jam’iyyar.
Kwamitin amintattun ya bayyana matukar damuwa game da halin da PDP ke ciki, musamman game da tsarin gudanarwa da yanke shawara na kwamitin zartarwa na jam’iyyar. Ya bukaci kwamitin zartarwa da ya gaggauta daukar matakin maido da jituwa cikin gida, hadin kai, da amincewar jama’a ta hanyar bin kundin tsarin mulkin PDP, gami da bin tsarin karba-karba na mukaman jam’iyyaar ga dukkan sassan kasar nan.
“Muna bukatar kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP ya mutunta tsarin mulki da ka’idojin jam’iyyar, wadanda suka kasance ginshikin nasararmu a baya,” in ji sanarwar kwamitin amintattu.
Kwamitin amintattu ya kuma yi Allah wadai da dage taron kwamitin zartarwa na kasa da aka yi, inda ya bayyana shi a matsayin cin amana a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
Kwamitin ya dage cewa taron kwamitin zartarwar wanda yanzu aka shirya yi a watan Fabrairun 2025, yana mai gargadin cewa duk wani karin dage taron zai iya kara tsananta kalubalen da ake da shi da kuma haifar da yamutsi ga jam’iyyarmu.”
“Dole ne kwamitin zartarwar ya nuna shugabanci na gari ta hanyar kiran wannan muhimmin taro kamar yadda aka tsara. Ba wai kawai cika alkawari ba ne, har ma da matakin da ya dace don warware matsalolin da ke damun jama’a da kuma tsara kyakkyawar turba ga PDP,” in ji kwamitin amintattu.
Babban abin da ya fi daukar hankali a cikin kudirorin kwamitin amintattu shi ne, umarnin da ya bayar ga masu ruwa da tsaki a yankin arewa ta tsakiya da su yi taro cikin gaggawa tare da gabatar da wanda zai maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Iyorchia Ayu.
Ko da yake Ambasada Iliya Damagun, ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a yankin arewa, inda daga bisani ya zama shugaban riko na jam’iyyar na kasa bayan korar Ayu daga rugujewar shugabanci wanda ya kara dagula rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar.
Kundin tsarin mulkin jam’iyya ya tanadi cewa a duk inda aka samu barin mukami a ofishin jam’iyya na kasa, sai wani daga shiyyar ya maye gurbin jami’in.
Da yake mayar da martani kan kudirin kwamitin amintattu, tsohon sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya yaba wa kwamitin bisa bai wa yankin arewa ta tsakiya umarnin gabatar da wanda zai maye gurbin Sanata Ayu.
Ya ce matakin ya yi daidai da bukatar shiyyar Arewa ta tsakiya wanda a ko da yaushe ke tada hankali kan cewa shugaban riko na kasa, Ambasada Umar Ilyasu Damagum ya koma kan mukamin da aka zaba na mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa tare da barin arewa ta tsakiya ta samar da magajin Ayu.
“Wannan matakin da kwamitin amintattu abun yaba ne sboda ya dace da matsayin jam’iyyar,” in ji tsohon sakatarenmai magana da yawun na jam’iyyar.