Kwamitin Ladabtarwa da Ƙorafe-ƙorafen Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
A hukuncin da kwamitin ya yanke a ranar Laraba, ya ce ƙorafin Akpoti-Uduaghan, wanda ke zargin Akpabio da cin zarafi da yin amfani da muƙaminsa ba daidai ba, ba shi da inganci saboda ita da kanta ta sanya hannu a takardar ƙorafin maimakon wani.
- Eric Chelle Ya Sake Bai Wa Ahmed Musa Damar Taka Leda A Super Eagles
- Natasha Da Akpabio: Sanata Natasha Ta Gabatar Wa Majalisar Dattawa Ƙorafinta
Haka kuma, kwamitin ya ce lamarin yana gaban kotu, don haka ba shi da ikon yin hukunci a kai.
Akpoti-Uduaghan, wacce ke wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya, ba ta halarci zaman sauraron ƙorafin ba.
Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya nuna takaicinsa kan rashin halartarta, yana mai cewa an sanar da ita.
A gefe guda, Akpabio ya musanta duk zarge-zargen da ta ke yi masa, yayin da Majalisar Dattawa ta tura Akpoti-Uduaghan zuwa kwamitin ladabtarwa saboda taƙaddamar da ta shiga tsakaninta da Shugaban Majalisar kan batun sauya wajen zama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp