Kwamitin tantance makarantun gaba da sakatare masu zaman kansu na bogi da gwamnatin Jihar Katsina ta kafa, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ahmad Muhammad Bakori, da dakta Bashir Usman Runwan Godiya da dakta Aliyu Idris, sun yi wa shiyar ƙananan hukumomi Funtuwa dirar mikiya don wayar da kan al’ummar yankunan.
da yake jawabi a sakatariyar ƙaramar hukumar Funtuwa, shugaban kwamitin, Farfesa Ahmad ya bayyana cewa asarar da Jihar Katsina ke yi na guraben aiki da samun takardun bogi na makarantu masu zaman kansu ya sanya gwamnati Jihar Katsina ta sanya kafa kwamitin tare da zagayawa ƙananan humumomi da ke cikin jihar don wayar da kan al’umma kan illa wadannan makarantun.
A cewar Farfesa Ahmad, yanzu haka kwamitin ya gano makarantu gaba da sakatare masu zaman kansu sama da 30 a faɗin Jihar Katsina na bogi. Ya ce duk da ingantatun makarantu gwamnati Jihar Katsina ke da shi, amma al’umma na ci gaba da kai ƴaƴansu makarantu bogi.
- An Yanke Wa Mai Gadi Da Mai Dafa Abinci Hukuncin Kisa Kan Kashe Tsohon Kwamishina A Katsina
- ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
Nan take kwamitin ya nemi jin ra’ayoyin al’ummar kan matakin da gwamnatin za ta dauka kan makarantu bogi.
Sakatariyar ilimi ta ƙaramar hukumar Funtuwa, Hajiya Maryam Babajo ta bayyana cewa zuwan wannnan kwamitin ya ƙara wayar da kai dangane da abubuwan da ba a sani ba.
daga ƙarshe, kwamitin ya tabbatar da cewa zai miƙa dukkan shawarwarin da al’ummar yankin suka bayar gaban Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Malam ɗikko Raɗda don daukar matakin da ya dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp