Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kwanan Nan FCE Jama’are Za Ta Fara Aiki – Gwamnatin Tarayya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bada tabbacin cewa sabuwar kwalejin ilimi mallakinta da ke Jama’are za ta fara gudanar da aikinta nan ba da jimawa ba.

Daraktan manyan makarantu na Ma’aikatar ilimi ta tarayya, Mr Joel Ojo shine ya bada tabbacin a jiya Talata sa’ilin nan da ya jagoranci tawaga ta musamman daga ma’aikatar ilimin don dubawa tare da nazartar muhalli da shirye-shirye kan matsugunin sabuwar makarantar da ke karamar hukumar Jama’amare a jihar Bauchi.

Joel Ojo ya shaida cewar tawagar tasu ta ziyarci muhallin wucin gadin da za a fara aiwatar da harkokin kwalejin a ciki tare da gane wa idonsu katafaren filin da aka tanada domin gina matsugunin sabuwar kwalejin na dindindin, inda kawo yanzu ya nuna gamsuwarsu da tsare-tsaren da su ke akwai a kasa, sai ya bada tabbacin cewa makarantar za ta fara aiki nan kusa ba da jimawa ba.

“Muhallan da su ke a kasa yanzu haka sun yi, filin da harabar duk sun yi. Aikinmu shine mu duba mu gani mu kuma kai rahoton ga shugabanmu.” A cewar shi.

Da ya ke magana a madadin al’umman karamar hukumar Jama’are, Shugaban kungiyar bunkasa Jama’are (JDF) Architect Sani Gidado, ya nuna matukar farin cikinsu da godiyarsu wa Gwamnatin tarayya a bisa amincewa da zaunar da kwalejin a yankin nasu.

Sani Gidado wanda kuma shine Marafan Jama’are, ya nuna cewa samar da sabuwar kwalejin za ta bada gagarumar dama wajen samar da aiyukan yi ga jama’an karamar hukumar tare da bunkasa harkokin ilimi a yanki, jihar Bauchi da ma kasa baki daya.

“Mu na kara gode wa Gwamnatin tarayya bisa kawo wannan kwalejin Jama’are. Ministan ilimi Adamu Adamu ya taka rawa sosai wajen baiwa Shugaban kasa Muhammad Buhari shawarar da har ta kai Jama’are ta samu wannan kwalejin, don haka muna godiya na musamman garesu.

“Samar da wannan kwalejin zai taimaka wajen kyautata harkar ilimi a illahin shiyyar arewa maso Gabas da ma kasa baki daya.

“Al’umman Jama’are suna cike da murna da annashuwa bisa hakan. Daga cikin alfanun samar da irin wannan kwalejin ga al’umma, za a samu damar da al’ummarmu za su sami aikin yi kama daga masu gadi, masu shara, da sauran ma’aikata da dama, don haka akwai hanyoyi da daman gaske da jama’a za su ci gajiyar wannan kwalejin, uwa uba ga inganta harkar ilimi”. A cewar shi.

Wakilinmu ya nakalto cewar garin Jama’are na fama da karancin manyan makarantu duk da ci gaban da karamar hukumar Jama’are ta samu, wasu na ganin Gwamnatin tarayya ta ma yi nazarin wannan laamarin ne tare da amincewa da zaunar da sabuwar kwalejin ilimi a garin.
Advertisement

labarai