Jam’iyyar NNPP ta bayar da wata sanarwa a hukumance cewa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai sake yin takarar shugaban ƙasa ba a ƙarkashin jam’iyyar a zaɓen 2027 ba.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Agbo Major, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani ga kalaman Buba Galadima, wanda ya ce Kwankwaso zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar kuma zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027.
- Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP
- Dole Kwankwaso Ya Nemi Afuwarmu Kafin Ya Komo APC
Major ya ce jam’iyyar ta riga ta kori Kwankwaso da Galadima bisa zargin aikata laifukan cin amanar jam’iyya, don haka ba su da ikon magana da sunan NNPP, balle su wakilci jam’iyyar a duk wani sha’anin siyasa.
“Tun da daɗewa NNPP ta sallami Kwankwaso da Galadima, don haka ba su da hurumin magana da sunan jam’iyya ko amfani da ita a wajen neman wata kujera ta siyasa,” in ji shi.
Major, ya jaddada cewa ba kamar yadda aka ba Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa kai tsayNNPP Ta Ce Kwankwaso Bazai Kara Yi Mata Takarar Shugabancin Ƙasa a 2027
Salim Sani Shehu
Jam’iyyar NNPP ta bayyana a hukumance cewa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai sake yin takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar a zaɓen 2027 ba.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Agbo Major, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani ga kalaman Buba Galadima, wanda ya ce Kwankwaso zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar kuma zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027.
Major ya ce jam’iyyar ta riga ta kori Kwankwaso da Galadima bisa zargin aikata laifukan cin amanar jam’iyya, don haka ba su da ikon magana da sunan NNPP, balle su wakilci jam’iyyar a a duk wani sha’anin siyasa.
“Tun da dadewa NNPP ta sallami Kwankwaso da Galadima, don haka ba su da hurumin magana da sunan jam’iyya ko amfani da ita a wajen neman wata kujera ta siyasa,” in ji shi.
Major ya jaddada cewa babu maganar bai wa Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa kai-tsaye kamar yadda aka ba shi a zaɓen 2023, wannan karon hakan ba zai maimaitu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp