Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta yi watsi da rahotannin da ke cewa dan takararta na shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai yi wa Peter Obi na jam’iyyar Labour Party takarar mataimakin shugaban kasa.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Agbo Major ya fitar, ya ce ba a taba yin irin wannan tattaunawa da Kwankwaso ba.
- Fayemi Ya Taya Oyebanji Murnar Lashe Zaben Gwamnan Ekiti
- Masu Son Shiga Harkar Fim Su Riki Biyayya Da Kyau – Abba Harara
“NNPP ba ta taba cewa mai girma dan takararta na shugaban kasa, Injiniya Dakta Rabiu Musa kwankwaso zai iya yarda ya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ba.
“Rahoton yaudara ne kuma abin kunya ne ga babbar jam’iyyarmu, dan takararta na shugaban kasa, Kwankwaso da miliyoyin magoya bayanta a Nijeriya da na kasashen waje, kuma ya bukaci ‘yan jarida da su rika bin diddigin rahotanninsu kafin su buga su don gujewa rarrabuwar kai gabanin babban zaben 2023.
“A matsayina na mutum na jama’a, NNPP ta amince da tattaunawar kawance da jam’iyyar Labour da don ta karfafa zumunta da kuma bunkasa dimokuradiyyar kasa yayin da muke kokarin hada kai don samar da sabuwar Nijeriya wacce jam’iyyar za iya ta lashe zabe,” in ji Mista Major.
Cikin ‘yan kwanakin da suka gabata an yada rade-radin cewar tsohon gwamnan Jihar Kano, na iya amincewa ya yi wa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa don tunkarar zaben 2023.