Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Kwankwaso Ne Gwaninmu A Babban Zaben 2019 – Magoya Baya

by Tayo Adelaja
September 16, 2017
in LABARAI
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Wasu daruruwan matasa magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, sun jaddada goyon bayansu da cewa shi ne gwaninsu a babban zaben 2019 da ke tafe.

samndaads

Matasan da suka fito daga yankin arewacin jihar Adamawa, sun bayyana haka ne a wani taron neman goyon bayan jama’ar yankin da suka gudanar a garin Mubi, suka ce Kwankwaso suke bukata ya tsaya takarar shugabancin kasar.

Da ya ke jawabi a taron shugaban kungiyar magoya bayan Kwankwason a jihar Abubakar Muhammad Jada, ya ce Kwankwaso shi ne zabinsu a babban zabe mai zuwa, don haka suka taru domin neman goyon bayan jama’a.

Ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne kawai dan siyasar da yake da manufa ingantacciya wajen bunkasa tattalin arziki da samar da ci gaba na siyasa, kasancewar yana kwarewa ta kowane fanni.

Alhaji Bamanga Tukur shi ne shugaban kungiyar a yankin kananan hukumomin Adamawa ta arewa, ya ce suna da dalillai da dama da yasa suka yarjema kansu cewa Kwankwaso shi ne jarumin da zai cire musu kitse a wuta, domin jajirtacce ne.

Ya ce bisa kwarewa da jajircewar Kwankwaso yasa ake mishi lakabi da Sanatan Arewa, yace babu wani abu da ya shafi jama’ar arewa da Nijeriya da Kwankwaso bai nuna damuwarsa akai, don haka suna da dalilai da dama na neman goyon bayan jama’a.

“Mun yi amanna Kwankwaso shi ne daya tilo da zai share mana hawaye, wannan ya sa kungiyarmu ta yi tsayin daka sai mun kai ga gaci, sai mun tabbatar mun shigar da Kwankwaso Aso Rock a 2019 insha Allahu.” In ji shi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kashe Jami’in Dan Sanda: An Kame Mutane Da Dama A Adamawa

Next Post

An Rantsar Da Sabbin Shugabanin Kungiyar Lauyoyi A Bauchi

RelatedPosts

Jihar Yobe

Mata Biyu Sun Zama Alkalan Manyan Kotu A Jihar Yobe

by Sulaiman Ibrahim
4 seconds ago
0

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya rantsar da...

Mulkin Nijeriya 2023: Kudu Maso Gabas, Kudu Maso Kudu Suna Tattauna Yanzu – PANDEF

by Sulaiman Ibrahim
5 mins ago
0

Kungiyar ‘Pan Niger Delta Forum’, (PANDEF) a ranar Asabar, ta...

Ministan Cikin Gida

Ministan Cikin Gida Ya Yaba Da Aikin Ginin Gidan Gyaran Hali Irin Na Zamani Da Ake Yi A Kano

by Sulaiman Ibrahim
5 mins ago
0

Ministan harkin cikin gida na Tarayyar Nijeriya Abdurra'uf Arebeosola ya...

Next Post

An Rantsar Da Sabbin Shugabanin Kungiyar Lauyoyi A Bauchi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version