Kwanturolan da ke kula da Sashen Kasuwanci na Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Anthony Ayalogu, ya rasu.
An ce Ayalogu ya fara rashin lafiya a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a ranar Litinin.
- Muna Kan Kokarin Magance Matsalar Hauhawar Farashin Kayan Masarufi —Buhari
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnan Bayelsa Ya Ayyana Hutun Kwanaki 7 Ga Ma’aikata
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban na Kwastam din ya fita hayyacinsa, inda aka garzaya da shi Asibitin Sojojin Sama da ke Kano, inda aka tabbatar da rasuwarsa da misalin karfe 8:20 na daren jiya.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, AA Maiwada na sashin hulda da jama’a na NCS, ya ce, “Ya na kan hanyar zuwa wani aiki a hukumance, sai ya fara rashin lafiya da ya isa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, sai ya fita hayyacinsa. Duk kokarin da aka yi na ba shi kulawa ya ci tura domin ya rasu ne a ranar Litinin 17 ga Oktoba, 2022 a Asibitin Sojin Sama na Nijeriya 465 da ke Kano.
Ya kasance yana da shekaru 57.” Dan asalin karamar hukumar Onitsha ta Arewa da ke Jihar Anambra ne, Ayalogu ya yi karatun digiri na farko a fannin Botany a Jami’ar Fatakwal.
Ya shiga aikin Kwastam a ranar 24 ga Satumba, 1991 a matsayin Mataimakin Sufurtanda na Kadet.
Shugaban Hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya jajanta wa ‘yan uwa da abokan arziki na marigayi Ayalogu, inda ya ce za a yi kewarsa matuka.
“Muna addu’ar Allah ya bai wa iyalan Ayalogu kwarin guiwar jure wannan rashi nasu.”