Kwararru a fannin sufuri da kayayyaki sun bukaci gwamnati da ta saka hannun jari wajen bunkasa da inganta hanyoyin sadarwa tare da tura fasahohin da za su saukaka jigilar kayayyaki zuwa tashar jiragen ruwa da na kasa.
Kwararrun sun shaida hakan ne lokacin wani taron fasaha kan harkokin sufuri.
- Gwamnatin Tarayya Zata Gina Manyan Tituna Na Zamani A Abuja-Lagos Da Fatakwal-Lagos
- Tattalin Arzikin Teku Zai Samar Da Aiki Miliyan 350 Da Dala Tiriliyan 2.5 – NIMASA
Shugaban ‘African Marine Enbironment Sustainability Initiatibe (AFMESI)’, Dr. Felicia Chinwe Mogo, ta ce, dole ne gwamnati ta inganta tare da fadada hanyoyin sufurin motoci, layin dogo, da kuma hanyoyin ruwa domin hada manyan cibiyoyin masana’antu da kasuwanci da tashoshin sufuri domin saukaka harkokin jigila.
A mukalar da ta gabatar kan kalubalen sufuri a jiragen ruwan Nijeriya, ta ce, hanyoyin sufurin tsawon shekara da shekaru suna fama da matsalolin don haka akwai bukatar gwamnatin ta rungumi amfani da fasaha domin kawo sauyi.
“Ya kamata tashoshin jiragen ruwa su kasance suna da kyakkyawar alaka tsakanin sauran tashoshin jiragen ruwa da na kasa. Har ila yau, tashar jiragen ruwa tana aiki azaman musanya tsakanin hanyoyin sufuri na teku kuma yana da mahimmanci don hadawa daga yanayin zamani,”in ji ta.
Mogo ta ce Dubai tana matsayi na biyar a jerin manyan cibiyoyin jigilar kayayyaki a duniya bisa ga Cibiyar Ci Gaban Harkokin Jiragen Ruwa ta Duniya 2019 kuma ta shida a ingancin hanyoyin samar da ababen more rayuwa da ingancin sufurin jiragen sama ta rahoton gasar ta duniya na 2019.
Ta ce Nijeriya ta samu kyakkyawar hanyar sadarwa, dole ne gwamnati ta tabbatar da ci gaba, kirkire-kirkire, da inganta mafi aminci, inganci da ingantaccen tsarin kasuwanci.
Mogo ta kara da cewa wajen auna hanyoyin sadarwa ta tashar jiragen ruwa, kamata ya yi gwamnati ta kuma yi la’akari da lokacin sufuri da karfin hanyoyin sadarwa na teku da ma’aunin hanyoyin sadarwa da mahimmin aikin tashar jiragen ruwa.
Mogo ta kuma jaddada cewa, samar da Depot na kwantena na cikin gida (ICDS) a wurare masu muhimmanci a fadin kasar nan, domin gudanar da jigilar kaya, wanda ta ce hakan zai taimaka wajen rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa, da samar da hanyoyin sarrafa kaya masu inganci ga masu shigo da kaya da masu fitar da kaya.