Ɗan wasan baya kuma kyaftin na Super Eagles, William Troost-Ekong, ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa ta kasa da kasa a hukumance, wanda hakan ya kawo karshen wasannin da ya bugawa tawagar Super Eagles ta Nijeriya.
Shahararren mai fashin baki akan harkokin wasanni Fabrizio Romano ne ya sanar da labarin a yammacin Alhamis ta shafinsa na Twitter, Troost-Ekong, mai shekaru 30, ya yanke shawarar rataye takalman kwallonsa na kasa da kasa, a cikin shekara 10 da ya shafe ya na bugawa Nijeriya kwallo Ekong ya samu damar bugawa Nijeriya wasanni 83.
A lokacin da yake tare da tawagar kasa, ya samu lambobin yabo uku kuma ya wakilci kasar a manyan gasa biyar, wanda ya sa ya zama ginshiki a bangaren tsaron tawagar ta Super Eagles, jagorancinsa da jajircewarsa sun matukar taka rawar gani wajen samun nasarar Super Eagles.
Ritayar Ekong ta zo ne kasa da sa’o’i 48 bayan an saka shi cikin jerin yan wasa 54 na Eric Chelle a gasar cin kofin kasashen Afirka (AFCON) mai zuwa, wanda zai fara a Morocco daga ranar 21 ga Disamba, kodayake ya wakilci Netherlands a matakin matasa, Ekong ya zabi ya buga wa Eagles wasa kuma ya fara buga wasansa na farko a shekarar 2015 a lokacin wasan neman gurbin shiga gasar AFCON da kasar Chadi.














