Akwai wasu mutane 2, daya ya iya magana sosai, amma ya kan manta da maganar da ya fada, yayin da dayan ba ya son magana, sai dai duk wani alkawari da ya yi, zai yi kokarin cika shi.
A cikin mutanen nan 2 wanne ka fi so? Tabbas za a kulla abota tare da mutum na biyu ko? Saboda “Alkawari kaya ne”. Ba za a iya dogaro kan wani ba, idan ba zai iya cika alkawari ba.
Wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ta zama aminiyar kasashen Afirka, shi ne yadda suke iya dogaro da ita, wato yadda take kokarin cika alkawarin da ta yi.
Don tabbatar da gaskiyar maganar, za mu iya kwatanta alkawarin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi, a taron ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana a birnin Dakar na Senegal, a karshen shekarar 2021, da jawabin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi, wajen taron jami’ai masu kula da aiwatar da sakamakon taron ministoci na FOCAC, wanda ya gudana a kwanan baya, inda jami’in ya yi bayani kan yadda kasar Sin take kokarin cika alkawarinta.
A wajen taron Dakar, shugaba Xi ya ce kasar Sin za ta ba kamfanonin hada-hadar kudi na kasashen Afirka lamuni, na cin bashin da ya kai dala biliyan 10 cikin shekaru 3 masu zuwa.
Zuwa yanzu watanni 8 sun wuce, an riga an ba da lamuni na samun bashin da ya kai dala biliyan 3. Ban da haka, kasar Sin ta ba da rance na dala biliyan 2.5, don tallafawa kokarin gudanar da wasu manyan ayyuka a kasashen Afirka.
A taron da ya gudana a bara, shugaba Xi ya ce kasar Sin za ta yi kokarin shigo da kayayyakin kirar kasashen Afirka da darajarsu za ta kai dala biliyan 300 cikin shekaru 3. Sa’an nan cikin watanni 7 da suka wuce, kasar Sin ta riga ta shigo da kayayyaki na dala biliyan 70.6 daga Afirka.
Yayin da a nasu bangare, kamfanonin Sin sun zuba jari da ya kai dala biliyan 2.17 ga kasuwannin kasashen Afirka, cikin watanni fiye da 8 da suka gabata.
A fannin aikin kiwon lafiya, shugaba Xi ya ce cikin shekaru 3, kasar Sin za ta ba da tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 600 ga kasashen Afirka, haka kuma kamfanonin kasar da na kasashen Afirka, za su yi hadin gwiwa wajen samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 400.
Zuwa yanzu, wasu watanni 8 sun shude, kasar Sin ta riga ta ba da tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 189 ga wasu kasashe 27 dake nahiyar Afirka, kana kamfanonin kasar ta yi kokarin hadin kai tare da takwarorinsu dake kasashen Afirka wajen sarrafa alluran, inda karfinsu ya kai samar da alluran rigakafi kimanin miliyan 400 a duk shekara.
Sauran ayyukan tallafi da hadin gwiwa da kasar Sin ta yi alkawarin aiwatar da su a kashen Afirka, sun hada da gina babban ginin hedkwatar cibiyar kandagarkin cututtuka ta nahiyar Afirka, da sauran manyan asibitocin hadin gwiwa, da rage talauci, da raya bangaren makamashi mai tsabta, da aikin tsaro, da dai sauransu, duk ana kokarin ciyar da su gaba, kamar yadda kasar Sin ta yi alkawari a baya.
Me ya sa kasar Sin take dora matukar muhimmanci kan cika alkawari? Saboda babbar manufar kasar Sin ta fuskar hadin gwiwa da kasashen Afirka ita ce, “gaskiya, da daukar takamaiman matakai, da zumunta, da sahihanci”, gami da “dora muimmanci kan adalci maimakon moriya”.
Kana Sin ta tsara wannan manufa ce bisa tushen akidarta ta “al’ummar dan Adam mai makomar bai daya”.
A ganin Sinawa, dole ne a yi kokarin tabbatar da ci gaban harkoki a kasashe daban daban, kafin a iya tabbatar da makomar bai daya mai haske ta daukacin dan Adam.
Wannan akida ta sa kasar Sin ke nuna cikakken sahihanci ga kasashen Afirka, da kokarin cika alkawarinta, yayin da take hulda da su. (Bello Wang)