Jam’iyyar Labour (LP) ta yi kira da a soke zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar Ribas.
A cewar jam’iyyar Labour, ta yi matukar kaduwa da labaran da ke fitowa daga jihar Ribas bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar.
Wata sanarwa da shugaban jam’iyyar Labour ta kasa Barr Julius Abure ya fitar, ta ce ‘yan bangar siyasa da ake kyautata zaton gwamnatin jihar ne suka turoso, sun mamaye rumfunan zabe da wuraren tattara sakamakon zabe, inda suka kwace kayan zabe da suka hada da takardar sakamakon zabe, suka daura sakamakon zabe na jabu a na’urar BVAS.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp