Hukumar kwallon ƙafa ta Laliga da kungiyar Real Madrid sun yi Allah wadai da cin zarafi na wariyar launin fata da aka yiwa dan wasan gaban Barcelona Lamine Yamal a wasan El-Clasico na ranar Asabar a Bernabeu.
Faya fayen bidiyo sun nuna yadda wani ɓangare na magoya bayan ƙungiyar ta Real Madrid suke furta kalaman nuna wariya ga ɗan ƙasar na Sifaniya yayin da yake murnar cin kwallonsa a minti na 77 ta hanyar nuna sunansa a bayan rigarsa.
- Endrick Ya Jefa Kwallonsa Ta Farko A Real Madrid
- Yadda Barcelona Ta Nuna Wa Bayern Munich Kwanji A Gasar Zakarun Turai
Sanarwar da La Liga ta fitar ta ce “La Liga za ta kai rahoto nan take kan abinda ta kira cin mutunci da nuna wariyar launin fata da ‘yan wasan Barcelona suka fuskanta zuwa ga sashin kula da laifuka na rundunar ‘yan sanda ta ƙasar.
“La Liga ta yi Allah wadai da abin da ya faru a Santiago Bernabeu, kuma ta dage wajen ganin ta kawar da duk wata dabi’a ta nuna wariyar launin fata da kiyayya a ciki da wajen filayen wasa.
A makon da ya gabata an kama mutane huɗu bisa zarginsu da gudanar da wani kamfe na nuna kiyayya da wariyar launin fata a kan ɗan wasan Real Madrid Vinicius Jr.