Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana farin cikinsa da lambar yabo da Kamfanin LEADERSHIP ya ba shi na zama Gwarzon Gwamnan Shekara ta 2025, inda ya yi alƙawarin cewa, ba zai ɗauki wannan karramawa da wasa ba.
Gwamnan, wanda ya yi wa marigayi Shugaban Kamfanin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, addu’a da godiya saboda hangen nesansa na kafa kamfanin, da ya zama mai yada labaransa, ba a yankin Arewa kaɗai ba har ma a Kudancin ƙasar baki ɗaya.
- Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna
- Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
Gwamnan, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi wasiƙar lambar yabon a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekara ta 2025 a Fadar Gwamnati da ke Lafia, a jiya Laraba.
Gwamnan Sule ya ce irin wannan jaridar da ke kan gaba ta zaɓo shi a matsayin gwarzon gwamna, abun farin ciki ne sannan ya yaba wa kamfanin bisa tabbatar da sahihancin labarai da daidaitasu wanda hakan yasa ta bambanta ta da takwarorinta.














