Hukumar Kula da Dokokin Hanya ta Jihar Legas (LASTMA) ta rufe wani gidan casu mai suna Vaniti Club House da ke kan titin Adeola Odeku a Victoria Island bisa laifin karya dokar harkokin sufuri ta shekarar 2018.
A cewar LASTMA, an rufe gidan casun ne saboda ajiye motoci ba bisa ƙa’ida ba a gefen titi da kuma toshe hanyoyi, lamarin da ke haddasa cunkoso da barazana ga lafiyar jama’a. Wannan matakin ya samu jagorancin babban daraktan hukumar, Olalekan Bakare-Oki, tare da sashen ceto da tabbatar da doka.
- Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos
- Kwalara Ta Kashe Mutane 5 A Lagos, An Kai 60 Asibiti Ranga-Ranga
Hukumar ta ce wannan mataki na ɗaya daga cikin tsarin sabbin dabarun sa ido da aiwatar da doka a faɗin Legas, kuma gwamnatin jihar na da ƙudurin tabbatar da tsari, da tsaro, da ingantaccen tsarin zirga-zirga.
Shugaban LASTMA ya gargaÉ—i cibiyoyin nishaÉ—i, kamfanoni da jama’a da kada su yi katsalandan ga zirga-zirgar ababen hawa ko su haifar da haÉ—ari ga lafiyar al’umma. Ya kuma buÆ™aci mazauna Legas su riÆ™a kai rahoto idan akwai cibiyar taro da ke hana zirga-zirga ta layukan gaggawa na LASTMA.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp