Bayani A Kan Fari Da Baki Baki
Duk da kasancewar baki bai cika samun tagomashi wurin lissafta launuka masu dacewa da wuri a wajen masana ado ba, amma shi ne mafi fitar da kyawon falo fiye da fari zalla ko ruwan madara musamman idan aka duba launukan da aka fi yayi a wannan shekara ta 2022.
Tsara adon falo da launin baki yana da jan hankali fiye da sauran launuka musamman idan aka raba shi da ruwan toka ko ruwan bulu wanda bai rinu sosai ba.
Fari
Launin fari, launi ne da ba shi da farin jini a wurin galibin iyaye masu yara da yawa ko wadanda suke sha’awar ajiye dabbobin gida a tare da su, amma kuma yana cikin sahun gaba a cikin launukan da ba za a iya biris da su ba wurin kawata falo. Idan aka yi amfani da farin fenti a falo, za ka ga falo yana daukar ido musamman idan aka tsara adon falon da kayan kujerun da suka dace da launin, walau an yi musu fenti ko ba a yi musu ba.
Haka nan za ka ga falo ya kara fito da kyawonsa idan aka shafa farin fenti a bango da kuma farin darduma ko kafet.
Za mu kawo muku wadanda suka rage a mako mai zuwa cikin yardar Allah.
Da fatan za a biyo mu.
Mun samo daga: https://www. countrylibing.com/uk/