Connect with us

RAHOTANNI

Layyar Bana: Ga Tsadar Abinci Ga Ta Dabbobi Da Kayan Masarufi

Published

on

Layya dai wata ibada ce ta yanka dabbobi da suka soma daga rago, tinkiya, bunsuru (dantaure), akuya, sa, shanu ko kuma soke rakumi ko rakuma a ranar goma ga watan Zulhajji bayan saukowa daga Sallar Idi.

Layya dai ta samo asali ne tun lokacin Annabi Ibrahim Alaihis Salam Inda Allah ya umarceshi da ya yanka dansa watau Annabi Isma’il Alaihis Salam wanda daga baya kuma Allah ya musanya masa da rago.

Kowace shekara idan watan Zulhijja ya tsaya za ka ga ana ta kai-komo da Dabbobi musamman raguna da ya ke mafi yawancin mutane sun fi son su yanka raguna saboda su ne mafi girman lada ko kuma kyautar kudade ga yan uwa da masoya don  sayen dabbobin da za su yanka, saidai  shekarar bana ta zo da barkwanci wajen mutane tun kama daga ma’aikatan gwamnati yankasuwa zuwa yansiyasa a sanadiyyar rashin hada-hada wanda bayan matsin tattalin arziki ga kulle bakin Aljihun gwamnatoci ko kuma kauda kai ga irin yadda aka saba na taimakawa idan wannan lokacin ya kusanto amma yanzu sai aka fake da cutar nan da ta ke addabar duniya yanzu watau ‘Corona birus’ wanda ya sanya mutane ido-kifi-ido-bado saboda abinci za su saye ko dabbar layya?

Wakilinmu na jihar Kebbi ya zagaya kuma zanta da mutane daban-daban.

Malam Nasiru Mera shugaban makarantar Madarasatul Usman Bn Affan Littahfizul Kur’an da ke unguwar low-cost  a garin Argungu Wanda ya yi  tsokaci akan muhimmancin Layya inda ya ce “ita dai Layya  Sunna ce ta Annabi Ibrahim da Annabi Muhammad (SAW) Kuma wajibi ce ga duk musulminda ke da halin yi wacce saboda muhimmancin ta har Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya naya cewa “Duk Wanda ke da halin yin ta kuma ya ki, to kada ma ya zo masallaci”

Bisa ga yanayin da al’umma ta sami kanta ya yi kira ga mawadata wadanda suka yi niyyar zuwa aikin Hajji amma Allah bai nufa ba da su bayarda sadakar wadannan kudaden ga yan uwansu ko kuma su saya musu dabbobi don su yi Layya.

Daga karshe kuma ya yi Kira ga iyaye da su kula da irin yaran da yayansu ke ma’amala da su saboda wannan lokacin da muka sami kanmu a ciki ya gurbata ainun.

Wakilinmu ya a babbar kasuwar sayarda  dabbobi (Kara) ta Argungu  da ke jihar Kebbi ya zanta da Shugaban masu sana’ar dillancin dabbobi na karamar hukumar mulki ta Argungu Malam Hussaini Garba Argungu ya kuma bayyana masa da cewa sama da shekaru talatin da biyar yana wannan sana’ar amma bai taba cin karo da shekarar da ta zo da matsala ba irin bana.

Ya ce bana ba ciniki saboda rashin kudi hannun mutane saboda ga dabbobi musamman raguna amma ba masaya, idan ka duba za ka ga mafi yawancin mutanen da ke wannan kasuwar sun kawo dabbobin ne don su sayar wanda mafi yawancin su duk suna sayarda dabbobin ne akan faduwa ba maganar riba inda har ma da kudin da aka sayi ragon ba su dawo ba duk da ya ke a wannan shekarar an fi kawo dabbobi inda farashin ragunan da ya sayar ya soma daga dubu arba’in zuwa dubu dari da saba’in.

Malam Hussaini Garba ya yi Kira ga gwamnati da ta taimakawa yansiyasa da ma’aikata kamar yadda aka saba a baya don hidimar Sallah wanda ta haka ne su kuma za su zo su sayi dabbobi.

Malam Sani Ibrahim wani malami ne da ke koyarwa a wata makarantar gaba da sakandare da ke jihar Kebbi, ya koka bisa ga irin wannan yanayin da al’umma ta sami kanta na matsin tattalin arziki wanda ya sanya wadansu turaddain samun sukunin sayen dabbar Layya.

Ya yi kiraga gwamnatin jihar ta Kebbi da ta waiwayi al’umma ta tausaya ta yi yadda gwamnatocin baya ke yi na bayarda kyauta ga yansiyasa don sayen dabbobi yayinda su kuma ma’aikatan gwamnati ko dai a ba su rancen albashi wanda za su iya biya cikin wadansu watanni ta hanyar cire wani kaso daga albashi.

Malam Aliyu Muhammed Kangiwa (KASPY)  wani magidanci ya bayyana cewa ya dauki tsawon shekaru yana Layya amma dai bana akwai matsala saboda akwai dabbobi sosai sanadiyyar mutane sun shiga sana’ar kiwo amma dai kash shekara ta zo da matsala inda ya ce ya zo da naira dubu saba’in da kudurin sayen raguna biyu amma abin ya faskara saboda kudin ba za su isa ba sai da ya nemo karin dubu goma ya hada sannan ya sayi raguna biyu Daya akan dubu arba’in dayan Kuma akan dubu arba’in da biyu duk da haka dai kanana ne sabanin shekarar da ta gabata inda ragon naira dubu talatin za a iya Layya da shi kuma yana da girma.

Malam Sani Tiggi (Sani Rewire) ya bayyanawa wakilinmu da cewa ba shakka wannan shekarar ta zo ta tararda al’umma cikin matsi wanda mutane da yawa ba za su iya sayen dabbar Layya ba saboda bayan ga tabarbarewar al’amurra ga kuma lalurorin iyali na yau da kullum wanda a cikin wannan halin ciyarda iyali ma ba karamin aiki ba ne, shi ma a halin da ake Allah dai ya kaddara yana kiwon rago da ya siya a baya amma da ya kawo wannan lokacin ba zai iya sayen dabbar Layya ba saboda mafi yawan lokaci tun safe har yamma sai dai a sami na kalaci wata rana ma sai dai a koma gida yadda aka zo.

Wani bincikenda wakilinmu ya gudanar musamman wajen malaman addini ya nuna mafi yawancinsu suna nuni da wadannan masifu da alummomi ke fuskanta ba ya rasa nasaba da halayensu na sabon Allah inda dukkansu sun yi ittifaki a kan janhankalin mutane da su ji tsoron Allah wajen ma’amalolinsu da mutane yan uwansu kuma su gyara tsakaninsu da Allah.
Advertisement

labarai