Daga Abubakar Abba,
Gwamnatin jihar Legas ta shelanta cewa tana yin dubi wajen habaka noma a jihar domin ba za ci gaba da yin dogaro kan jihohin Arewacin kasar nan domin samar da wadataccen abinci a jihar ba.
In za a iya tuna wa, Gwamnatin na mayar da martani ne kan dakatar da kai abinci zuwa Kudancin kasar nan daga Arewacin Nijeriya da gamaiyyar kungiyoyin safarar abinci da kuma dabbobi suka yi a kwanan baya, inda hakan ya janyo tashin farashin abincin da kuma dabbobi.
Kwamishiniyar ma’aikatar aikin gona ta jihar Abisola Olusanya ce ta shelanta hakan a taron bayar da horo na kwana biyar ga malaman gona da ya gudana a jihar.
Taron wanda aka gudanar dashi a jihar ta Legas, Hukumar Bunkasa Aikin Gona (LSADA) tare da hadin gwiwa da ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta jihar ce suka shirya shi.
Bugu da kari, manufar bayar da horon shi ne a karfafa wa malam gona kwarin gwiwa da kuma ilimantar da su kan yin aikin noma na zamani, inda alfanun zai koma kan manoman dake a jihar, musamman domin kara bunkasa samar da wadataccen abinci a jihar.
A cewar Kwamishiniyar ta ma’aikatar aikin gona ta jihar Abisola Olusanya, Legas ba za ta ci gaba da dogaro kan Arwacin Nijeriya ba wajen samun wadataccen abinci.
Kwamishiniyar ma’aikatar aikin gona ta jihar Abisola Olusanya ya ci gaba da da cewa, wannan abu ne dan lokaci, inda ta kara da cewa, hakan ne ya zaburar da Gwamnatin jihar wajen bai wa malam gona horo.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa, samun malaman da za su gudanar da hakan, ya zama dole a a karfafa masu gwiwa, inda kuma ta bukaci da a kara samar masu da dauki .
Abisola Olusanya ta ci gaba da cewa, “A matsayin ku na malaman gona, ba wai ana bukatar ku koya wa manoman aikin noma na zamani ba kawai ya kuma zama wajibi ku ilmantar da manoman kan yadda amfanin gonar da suka noma su samu farashi mai kyau a kasuwa”.
Ta sanar da cewa, har ila yau hakan na nuna za ku koya wa manoman kasuwancin noma, musamman domin su samu kudin shiga masu yawa.
Abisola Olusanya ga su malam gonar, ya zama dole a ba ku kwarin gwiwa kan aikin da za ku gudanar da kuma samar masu da dauki.
Kwamishiniyar ma’aikatar aikin gonar ta ce, na lura da cewa, muna fuskantar karancin malaman aikin gona a jihar Legas, amma za mu kara zage damtse don kara samar da malaman da dama, musamman kan yunkurin da gwamnatun jihar ke kan yi na habaka aikin nomaa jihar da kuma yin amfani da fannin wajen kara bunkasa tattalin arzikin jihar da da kuma kara wadata jihar da abinci mai yawa da da kuma kasa baki daya.