Yusuf Shuaibu" />

Legas: Mutum Ya Gurfana A Kotu Bisa Lalata Da Diyar Kishiyar Mahaifiyarsa

An gurfanar da wani mutum a gaban kotun Ikeja da ke Legas mai suna Mista Michael Akintayo dan shekara 49 da haihuwa, bisa laifin yin lalata da diyar kishiyar mahaifiyarsa. Alkalin mai shari’a na kotun, Misis Olufunke Sule-Amzat, ta yi fatali da duk wani hujja da wanda a ke tuhuma Akintayo ya bayar, inda ta bayar da umurnin a cigaba da tsare shi a gidan yarin Kirikiri tare da bayar da umurnin a mika fayal din shari’ar ga ma’aikatar shari’a ta jihar. Ta kuma dage sauraron wannan kara har sai zuwa ranar 21 ga watan Oktoba.

Tun da farko dai, lauya ‘yan sanda mai gabatar da kara, ASP. Benson Emuerhi, ya bayyana wa kotu cewa, wanda a ke tuhuma ya aikata wannan laifi ne a tsakanin shekarar 2017 da kuma watan Afirilun shekarar 2019, a gidansa da ke Railway Compound cikin yankin Ebuta-Meta. Emuerhi ya zargi wanda a ke tuhuma da yi wa yarinya ‘yar shekara 13 fyade tun a shekarar 2017, inda ya fara saka mata hannu a gabanta.

Yarinyar ta bayyana cewa, wanda a ke tuhuma ya yi lalata da ita na karshe ne a cikin watan Mayu, lokacin da ya kira ta zuwa dakinsa, inda ya tunga saka mata hannu a cikin gabanta.

“Iyayen yarinyar sun kai korafi a ofishin kare hakkin Dan Adam, inda jami’an hukumar su ka tura karar zuwa wurin kwamishinan ‘yan sandar jihar, domin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin,” in ji lauya mai gabatar da kara.

Emuerhi ya bayyana cewa, wannan laifin ya saba wa sashe na 261 na dokar manyen laifuka ta shekarar 2015.

Exit mobile version