Shugaban kwamitocin majalissar dokokin Afirka ta Kudu Cedric Frolick, ya soki lamirin leken asirin kasashen waje, da ake zargin gwamnatin Amurka da aikatawa. Mr. Frolick ya yi tsokacin ne yayin zantawar baya bayan nan da ya yi da kafar CMG, yana mai cewa, hakan keta hurumin ‘yancin mulkin kan kasashen da abun ya shafa ne da suka hada da na Afirka.
A farkon watan nan ne dai wasu takardun bayanai, suka bulla ta kafofin sada zumunta, wadanda ke fallasa yadda Amurka ke leken asirin sauran kasashe, ciki har da kawayen ta, da ma wasu hukumomin kasa da kasa, da suka hada da MDD.
Takardun sun haifar da matukar damuwa ga kasashe da dama, ciki har da Afirka ta Kudu, wadda ke makwaftaka da Namibia, inda aka gano cewa wani jirgi maras matuki na Amurka, na tattara wasu bayanai ta samaniyar tekun Namibia, kusa da tekun Afirka ta kudun.
Game da hakan, a cewar dan majalissar, duk da cewa Amurka ta ce jirgin maras matuki ba mallakin gwamnati ba ne, kuma yana gudanar da ayyukan bincike ne a fannin zirga-zirgar ruwa, a hannu guda, wasu kafofin watsa labaran Namibia sun yi zargin cewa, jirgin na leken asiri ne kuma mallakin gwamnatin Amurka. (Saminu Alhassan)