Kwanan baya, wakilin babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin wato CMG ya zanta da masani a fannin ilmin injuna masu kwakwalwa Leslie Valiant, wanda ya lashe lambar yabo ta Turing a shekarar 2010.
A yayin zantawarsu, Mista Valiant ya bayyana cewa, Sinawa suna sha’awar yin nazari kan ilmi a ko da yaushe. Kasar Sin tana da al’adar yin nazari kan ilmi, lamarin da ya kasance abu mai amfani sosai. Haka kuma, ya ce, a halin yanzu, kasar Sin tana dukufa wajen raya ilmin lissafi da kimiyyar injuna masu kwakwalwa da kuma ilmin kimiyya na tushe, lamarin da ya kasance abin yabo. Kana, ya yi imanin cewa, kasar Sin za ta cimma nasara da samun sakamako mai kyau, inda ya kuma nuna yabo ga al’adar kasar Sin ta son yin nazari kan ilmi, kamar ilmin lissafi da sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp