Babban mai shigar da kara na Libya ya ba da umarnin a tsare jakadiyar kasar a Brussels a ranar Talata bisa zargin cin hanci da rashawa, jim kadan bayan da gwamnatin Tripoli da kasashen duniya suka amince da sallame ta.
An yi wa Amel Jerry tambayoyi game da “cin zarafin gwamnati da na kudi” da ake zargin an yi amfani da ita don “samun fa’idar haram ta hanyar kwace dukiyar jama’a ba bisa ka’ida ba da kuma cutar da muradun jama’a”, in ji ofishin mai gabatar da kara Al-Seddik al-Sour.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Kashe Kansila A Katsina
- Cire Tallafin Fetur: Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Abinci
Da yake lura da “dacewar shaidar” kan jakadiyar, Al-Sour ya tuhume ta tare da ba da umarnin tsare ta na wucin gadi, in ji ofishin a cikin wata sanarwa, ba tare da bayyana inda ta ke ba.
Tun da farko gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a yammacin Libya ta sanar da korar Jerry ba tare da bayar da wani bayani ba.
Kasar Libya mai arzikin man fetur ta fada cikin rikici tun bayan boren da mutanen kasar suka yi a 2011 wanda ya hambarar da gwamnatin shugaba Moamer Gadhafi, kuma cin hanci da rashawa ya yi kamari a cikin cibiyoyin gwamnati.
Kasar da ke arewacin Afirka ta kasance cikin rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnatoci biyu masu gaba da juna, daya a Tripoli da kuma daya a gabashin Libya da ke samun goyon bayan wani babban soji Khalifa Haftar.
Batun cin hanci da rashawa na baya-bayan nan ya barke ne bayan da aka yada wani faifan murya da aka danganta shi da Jerry a shafukan sada zumunta.
A cikin faifan bidiyon, ana iya jin wata mace tana magana wadda aka bayyana a matsayin sakatariyarta, tana mai da’awar cewa tana bukatar “rasitan karya” na sama da Yuro 200,000 (dala $209,000) don maganin cutar kansa ga wani majiyyaci na Libya.
Sakatariyar ta tabbatar da sahihancin faifan bidiyon ga kafafen yada labarai na Libya.
A cikin faifan bidiyon, matar ta ce dole ne a aika da daftarin zuwa ma’aikatar lafiya ta Libya don samun amincewarta na sakin kudaden.
Biyan kudaden jinya ga ‘yan kasar Libya a kasashen waje, daidaitacciyar al’ada ce ga wakilan kasashen duniya na Libya, amma jami’ai a kai a kai suna yin tir da rashin bin ka’ida.
A cewar jaridar Le Soir ta kasar Belgium, ana kuma zargin Jeary da “shakku” wajen mika kudaden al’ummar Libya da ya kai dubunnan daruruwan daloli, zuwa wani kamfani mallakar danta.
Rahotanni daga kasar Belgium na cewa jakadiyar ta koma kasar Libya, sai dai kawo yanzu babu tabbacin hakan.