Chijioke Anekpo wani kwararen likitan kunne,hanci da makogwaro ne wanda kuma daga Jihar Enugu ce yake sashen Kudu maso gabashin Nijeriya ya yi karin bayani ne kan illar da mutum wanda ke da dabi’arnan ta goge kunnuwansa wanda akasarin mutane suka saba yi da sunan ai suna tsaftace kunnuwansu ne.
A hirar da aka yi da shi Anekpo ya yi kira ne da mutane da su bar irin ita dabi’arnan ta sa auduga a kunnuwansu da sunan suna tsaftace su, saboda a sanadiyar yin hakan suna iya fuskantar matsalolin da suka shafi lafiya.
- An Fara Ginin Katafariyar Tashar Samar Da Lantarki Daga Hasken Rana Da Kafin Iska A Arewacin Kasar Sin
- NIS Ta Bankado Sabbin Dabarun Da Masu Safarar Mutane Ke Amfani Da Su A Jihar Bayelsa
Anekpo yace hakiaka akwai illa sai dai yin hakan ya danganta ne da yawan karar sautin da mutum ke ji ne.Yin haka da yawa ka iya yi ma kunnuwan mutum illa.
Bugu da kari kuma ya yi karin haske akan wasu abubuwan da suke jawo matsalar data shafi lafiya ga kunnuwan mutane da kuma na wadanda basu kawo matsala.
Sai dai yace” Babu wata matsala idan ruwan sabulu ya shiga cikin kunnuwan mutum lokacin da yake yin wanka,domin koda ruwan ya shiga cikin kunnuwan mutum yana fita da kansa bayan wani dan lokaci.
Ya kara da cewar bai dace a rika goge kunnuwa ba domin kuwa sanin kunne wani bangare ne na jikin mutum ne, don haka kokarin da za ayi na tsaftace su kansa, a kaiga shiga wata matsala, koda-yake, ba kowa ne ya san da hakan ba.
Yace mutum zai iya goge daga wajen kunnuwansa amma ba ciki ba saboda illar dake tare da yin haka.
Likitan ya kara da cewa ya dace daga haihuwa har ya zuwa ranar da mutum zai koma ga mahaliccinsa kar ya goge cikin kunnywansa musamman ma da auduga.Saboda ana iya samun matsala a wasu lokuttan inda audugar na iya makalewa a cikin kunnuwan mutum ta samar masu da matsala.
Wani abu kuma daban Dokta Anekpo yace ruwan sanyi na iya cutar da mutum idan har bai saba da yin hakan ba wato shan shi.
Shan ruwan sanyi ga da bai saba ba na iya sa mutum ya kamu da cutar tari ko mura.
Ya kara da cewa babu illa amma a tabbatar da cewar shi ruwan bai da zafi sosai domin idan akwai aka sha zai iya kona baki.
Gashin hanci ai yana taimakawa ne wajen kare datti ko kuma kurar da mutum zai iya shaka, bai kamata a rika aske gashin dake cikin hanci ba amma ba laifi bane a rage tsawon gashin.
Bugu da kari ashe irin al’adarnan ta cire Tasono ma wata illa ce domin yawan cire tasonon daga hanci ne ke sanadiyar kamuwa da Habo.
Anekpo ya kara da cewar da akwai matukar illa amma ga wadanda suke fama da cututtukan da suka hada da huhu da zuciya baya ga haka takunkumin fuska ba shi da illa ga lafiyar mutum.
Hayaki musamman daga abubuwan hawa yana cutar da lafiyar mutum domin a cikin hayakin akwai sinadarin ‘carbon monodide’ wanda ke cutar da zuciya da huhu.