Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home ADABI

 Littafin ‘SAI YANZU’ Na Hanne Ado Abdullahi (1)

by Muhammad
April 6, 2021
in ADABI
5 min read
Littafin
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tsohuwar mota kirar ‘yar kurkura ke tafe a kan titin Zaria Road. Ko’ina na motar shake yake da kayan gini. Hatta inda fasinjojin motar suke zaune, su da wasu manyan bokitan fenti ne takure a kan kujerar. Ita kanta motar dakyar take tafiya, alamun kayan da aka dora mata sun fi karfinta. Daga dukkan alamu kayan da ta dauka sun nunka ta a nauyi, kusan duk inda ta wuce, sai ta barwa duk abin da ta wuce tsarabar farin hayaki. Duk wanda ta gitta ta kusa da shi  kuwa, sai ya nuna kosawa da rabar sa da ta yi. Amma sam ga dukkan alamu fasinjan motar ba abin da ya dame su. Yadda motar take tafe a hankali mai nuna alamun zata iya tsayawa a ko da yaushe bai dame su ba.

Hirar su kawai suke yi. Ga shi dai yanayinsu daya da motar mai nuna alamun wahala, amma hakan bai nuna ba sam a fuskokinsu. Mallam Musa ke nan  da Mallam Jibrin. Matasa ne masu kimanin shekaru talatin zuwa talatin da biyu. Ba ‘yan gari daya ba ne, amma makotaka da juna ta sa sun zama fin ‘yan uwa. Tun Mallam Jibo na da kimanin shekaru bakwai aka kawo shi karatu daga can wajen Mambila ta jihar Adamawa, yayin da shi kuma Mallam Musa ya kasance dan kauyen Dagumawa a cikin karamar hukumar Wudil ta jihar kano. Shi kam ba karatun allo ne ya kawo shi ba, wansa ne da suke uwa daya uba daya ya dauko shi, bayan rasuwar iyayensu da suka rasu sanadiyyar hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyarsu ta dawowa daga barkar dan babban dansu. To a nan ta Allah ta kasance a kansu.

Wannan dalili ya sanya yayan Mallam Musa ya dauko shi ya dawo da shi wajensa a kan zai taho da shi Kano ya sanya shi babbar makaranta lokacin yana kimanin shekaru goma sha biyu, amma hakan ya gagara. Sai shi da kan sa ya kai kansa makarantar allon da Mallam Jibo yake. Halin su ya zo daya, saboda dukkansu mutane ne marasa son tashin hankali ga su da amana da hakuri. Shi Mallam Jibrin alamajiranci ya kawo shi Kano, shi kuma Mallam Musa zumuncin zamani ya kawo shi. Hakan ya sanya yanayin rayuwarsu ya zama iri daya.

Da farko sana’ar wanki da guga suke yi, kuma har a wannan lokaci itan dai suke yi. Da kuma hakan suka kukuta suka gina ‘yan gidajensu daura da juna.

Hakurin da kuma biyayyar mallam Musa ya sanya yayansa ya mayar da shi kamar bawa. Duk wata wahalarsa shi yake sakawa ya yi masa, amma fa matsala ko ta sisin kwabo ba zai maganta ma sa ba. Idan kuwa aiken kudi ya hada su ya dinga yi masa bin kwakkwafi ke nan. A lissafa a sake lissafawa. Amma duk da haka idan aka gama sai ya nuna masa cewar hakura kawai ya yi, amma tabbas sai ya nuna shi fa an cuce shi.

Honourable Iliyasu Dagumawa ke nan. Shi dan siyasa ne kuma siyasar tana kai masa. Tun da har mukamin chairman na wudil Local Gobernment ya taba rikewa. Kuma har a yanzu duk wanda yake neman kuri’a daga nan shiyyar sai sun tsaya masa zai samu, saboda haka ya kasance babba a duniyarsu ta siyasa.

Amma fa ba wanda ya san ana yi sai matarsa da ‘ya’yansa.  Rana guda Mallam Musa ya ware ta yin wanki da gugar gidan honourable, ya sai sabulu da kansa ya sai ruwa idan na famfon ya dauke, amma ko godiya bai taba samu ba. Kazalika abokin sana’ar sa bai taba kosawa da taimaka masa wajen hidimar yayan nasa ba. Duk jagwal din da ya saka su haka zai taimakawa amininsa su yi tare.

A yanzu haka wannan kayan ginin na gidansa ne da ake yiwa gyara. Kyat da kyat haka ya ba su kudin sayen kayan, bayan wahalar da suka sha na zagawa wajen nemo masa farashin kayan.

Sun je kasuwa ya kai sau biyar a kan wannan sayayyar, amma ko kudin mota bai taba hada su da shi ba. Yanzu ma kuma da ya dora musu wahalar sayen kayan gini haka ya bar su babu kudin lodi dana mota. Haka suka loda kayan da kansu suka kuma biya kudin mota daga aljihunsu. Shi in dai mutum ya ci kudinsa, to kuwa dan jagaliyar siyasa ne. Ya rabo shi da iyayensa, makaranta da ya yi alkawari saka shi bai ba shi damar yin ta ba, sai uwar bauta da ya dora masa. Haka Mallam Musa yake fama da wahalarsa, masifar matarsa mama, da kuma rashin kunyar samarin ‘ya’yansa guda biyu, da suka mayar da shi kamar yaron gidansu. Ga shi dai ya girmi babban da sama da shekaru sha biyar domin sanda ya zo gidan ma  Amir na shekararsa ta farko balle Sadam da ya gaza shi da shekaru uku ba. Amma dukkanninsu ma ba girma su ke bashi ba. Shi kam Sadam ma da yake wawa wawa ne sai da ya kai shekaru goma san nan ya san cewa Mallam Musa Baffansa ne. Mai dan dama a cikin su ita ce Amira. Ita bata da rashin kunya kamar sauran yayyenta.

Honourabla Iliyasu na zaune a unguwar Hotoro NNDC, yayin da Mallam Musa da kuma amininsa Mallam Jibrin suke zaune a nan gangaren unguwa uku. Gidajensu ba wani girma ne da su ba. Suna nan kamar na talakan birni. Dakuna ne kanana guda biyu daga cikin gidan. Sai dan karamin tsakar gida mai dauke da karamin bayan gida da kuma dakin girki. Akwai karamin daki mai kallon kofar gida da kuma kofa biyu, daya ta ciki daya kuma ta waje. Wadannan dakuna guda biyu daya daga gidan Mallam Jibrin daya kuma a jingine da shi daga gidan Mallam Musa a nan suke ajiye kayan gugar mutane kafin su zo su karba. Haka zalika idan bako daya daga cikinsu ya yi. Nan din dai za a tattare kayan sana’a bakon ya sauka a ciki. Shi Mallam Musa yana zaune da matarsa Ramatu da kuma dan matashin dansu Ahmad wanda suke kira Baffa saboda sunan mahaifin Mallam Musa aka saka masa.

Ita kuwa Ramatu matarsa ‘yar nan unguwa uku ce. Mahaifinta kafin rasuwarsa kayan miya yake sayarwa. Ita kadai ce ‘yarsu. Bayan rasuwarsa, matarsa Dada ta koma rugar iyayenta a can dajin Falgore, ita ma din kuwa ba ta fi shekara hudu da komawa ba ta rasu.

Shi kuwa Mallam Jibrin nasa iyalin akwai matsala. Sabanin Mallam Musa shi tasa matar ba a samu karuwar komai da Ita ba sai tsabar masifa, kwadayi, roko da kuma tsinannen yawo. Kullum tana hanyar gidan honourable. Duk irin wulakanci da matar gidan da ‘ya’yanta suke lafta mata bata gani. Ita dai burinta ta gwada wa ‘yan unguwa ta isa  ta shiga gidan Honourable. Tsawon shakaru goma da suka dauka tare ba haihuwa sai tsabar tashin hankali da yake samu daga wajenta. Hakan yayi sanadin rabuwarsu. shi ya sa ya koma gida can mayo lofe a can Mambila ya auro ‘yar uwarsa. Ganin ta shekara sama da uku ita ma Allah bai bata haihuwa ba, ya sanya Mallam Jibrin yarda da zagin da Matarsa Haule take yi masa na cewar rashin haihuwarta daga wajensa ne. Ya fara nuna damuwa da hakan amman matarsa Wabili ta karfafa  masa gwiwa da nuna masa haihuwa da rashin ta duk na Allah ne. Halinsu ya zo daya da Ramatu . A hankali ma Baffa ya koma dan gidanta. Balle da yanzu mahaifiyarsa ta ke fama da laulayin ciki, sai komai nasa ya koma wajen Wabili.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Kudaden Da CBN Ke Samarwa Za Su Bunkasa Tattalin Arziki

Next Post

FIM DIN GIDAN DAMBE A GIDAN DAMBE

RelatedPosts

Rubutu

Shiga Tsakanina Da Masoyina Ya Sa Na Fara Rubutu – Na’eemerh Sulaiman

by Muhammad
3 days ago
0

Fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, wacce ke sharafinta a yanar gizo...

Irin Ilimin Da Muka Karu Da Shi A Gidan Dambe Saboda Fim Din Gidan Dambe – Marubuta

Irin Ilimin Da Muka Karu Da Shi A Gidan Dambe Saboda Fim Din Gidan Dambe – Marubuta

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Daga Maje El-Hajeej Hotoro, Kano A makon da ya gabata,...

TSARABAR RAMADAN: Rubutacciyar Waka Daga Abdulhamid Maluman Matazu

TSARABAR RAMADAN: Rubutacciyar Waka Daga Abdulhamid Maluman Matazu

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Gabatowar watan Ramadan, wanda al'ummar musulmi ke azumtar dukkan ranakun...

Next Post
Dambe

FIM DIN GIDAN DAMBE A GIDAN DAMBE

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version